Home / Labarai / Sojojin Najeriya Sun Ceto Tsohon Shugaban Kwalejin Ilimi Da ɗansa A  Zamfara

Sojojin Najeriya Sun Ceto Tsohon Shugaban Kwalejin Ilimi Da ɗansa A  Zamfara

Daga Imrana Abdullahi
A kokarin ganin sun magance matsalar masu rike da bindiga ba tare da izini ba suka ta’addanci da satar mutane suna neman kudin fansa, Rundunr sojin Najeriya ta ce kubutar da tsohon shugaban kwalejin ilimi ta tarayya da ke Gusau Dakta Hassan Abubakar Augie tare da ɗansa daga hannun masu garkuwa da mutane.
Cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar a shafin ta na Tuwita, su ce  dakarunsu na rundunar Hadarin Daji da ke Mada ne suka kubutar da Dakta Augie tare da ɗansa a lokacin wani sintiri da suka gudanar  a kan hanyar Shemori zuwa Yandoto.
Sanarwar ta ce dakarun sun fatattaki ‘yan bindigar masu yawa, inda suka yi musayar wutar da su.
Sojojin sun ce ‘yan bindigar sun gudu zuwa cikin daji bayan da suka ji wuta daga ɓagaren sojojin, tare da barin mutanen biyu da suka sace.
Binciken farko ya nuna cewa an sace mutanen biyu ne a daren ranar Alhamis a gidan Dakta Augie, inda aka ta fi daji da su kuma suka ci gaba da tsare su, har zuwa lokacin da sojojin suka isa wajen.
Sojojin sun kuma samu nasarar ƙwato babura biyu na ‘yan bingidar a lokacin gumurzun.
Jihar Zamfara dai na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da rikice-rikicen ‘yan bindiga da ke sace mutane domin neman kudin fansa

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.