Home / KUNGIYOYI / Kungiyar Mawallafa Ta Karrama Maryam Suleiman Mai Rusau

Kungiyar Mawallafa Ta Karrama Maryam Suleiman Mai Rusau

Daga Imrana Abdullahi

Sakamakon irin kokarin ganin rayuwar mata da kananan yara ta inganta musamman a bangaren hada hadar harkokin siyasa ya sa shugabar matan jam’iyyar APC Hajiya Maryam Suleiman da ake yi wa lakabi da mai Rusau hakan ne yasa kungiyar Mawallafa Mujallu da Jaridu suka Karrama ta da gagarumar lambar karramawa.

A wajen wani gagarumin taron da aka yi na mata a ofishin jam’iyyar na Jihar Kaduna bayan karbar lambar karramawar Hajiya Maryam Suleiman da ake wa lakabi da Mai Rusau ta bayyana cikakken gamsuwar ta da wannan lambar karramawar da aka ba ta daga kungiyar Mawallafa ta “Arewa Publishers Forum”

“Hakika na ji dadi kwarai da wannan karramawa da aka yi Mani bisa irin la’akari da aka yi na kokarin rungumar daukacin matan jam’iyyar APC a Jihar Kaduna.

Kuma a matsayina na shugabar mata a jam’iyyar APC ina karfafa wa mata Gwiwar cewa Gwamnatin APC a shirye take ta saka masu da hanyar yi masu abubuwan alkairi n da zai taimaka masu da yayansu baki daya.

A saboda haka ne nake yin kira ga daukacin mata da sauran al’ummar Najeriya baki daya da su ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga matakan Gwamnati uku da kuma dukkan zababbu a karkashin jam’iyyar APC wanda hakan zai bayar da damar dukkan zababbu su kara kaimi wajen aiwatar da ayyukan alkairi a kasa baki daya.

” ina son daukacin mata a ko’ina suke su kara nunka irin hadin kai da goyon bayan da suke ba Gwamnatin APC tun daga matakin kananan hukumomi, Jihohi da kasa baki daya saboda hakan zai ba Mata da yayansu damar cin ribar muhimman ingantattun tsare – tsaren ciyar da jama’a gaba da Gwamnatin APC ke aiwatarwa a kowa ne matakin Gwamnati, haka nan ma ina jaddawa Mata da yayansu cewa ba za a barsu a baya ba wajen samun damar cin ribar Dimokuradiyya a Najeriya.

Ina godiya da wannan karramawa da aka yi masu da lambar karramawa mai muhimmanci daga muhimman mutane a kasa.

Tun da farko a jawabinsa shugaban kungiyar Mawallafa mujallu da jaridu na kasa Dikta Sani Garba cewa ya yi a gaban yaron matan da suka taru a wajen taron cewa Hajiya Maryam Suleiman ta ciri tuta ne sakamakon irin kwazon aiki da nufin inganta rayuwar Mata a kowane irin mataki baki daya.

Sani Garba ya ce “mun yi duba sosai da irin ayyukan da Hajiya Maryam Suleiman da ake yi wa lakabi da Mai Rusau take yi wajen inganta rayuwar jama’a Maza da Mata yara da manya don haka muka yanke hukuncin bayar da wannan karramawar da Gwarzuwar Mace da ta ciri tuta a tsakanin al’umma

A dai cikin ofishin ta da ke harabar ofishin jiha na jam’iyyar APC mun ga irin yadda jama’a da dama kowa ke murna da jinjina ga Hajiya Maryam Suleiman Mai Rusau da lambar karramawar da aka ba ta.

Ko a ofin nata mun ga wata hadaddiyar kungiyar Badarawa, Malali da Kwaru Forum sun Karrama Hajiya Maryam da lambar karramawa mai taken ” Hajiya Maryam Pillar of hope”, wanda hakan na nufin mai kokarin inganta rayuwar matasa galihu kenan wanda daman aikin da aka Santa da shi kenan a tsakanin Mata da a koda yaushe ta ga rayuwar Mata da yayansu na cikin walwala da jin dadi baki daya.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.