Daga Imrana Abdullahi
Bayanan da muke samu daga Jihar Kaduna na bayanin cewa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Muktar Ramalan Yero ya fice daga jam’iyyar PDP.
Kamar dai yadda wakilin mu ya ga wata takardar da ya rubutawa mazabarsa ta Kaura ya na shaida masu cewa ya fice daga jam’iyyar PDP .
Kuma kamar yadda muka ga takardar hakika shugabannin PDP na mazabar Kaura a cikin birnin Zariya na Jihar Kaduna sun ga wannan takardar.
Wakilin mu ya tuntubi wani daga cikin hadimansa ko takardar da muke gani gaskiya ce sai ya tabbatar mana cewa hakika haka maganar take kuma ya san da ita saboda haka gaskiya ce wannan batun ficewa ta tabbata gaskiya.
Amma dai har yanzu bai bayyana inda zai koma ba.