Home / News / Kansilolin PDP 19 Tare Da Magoya Bayansu Dubu Hamsin Sun Koma APC A Kaduna

Kansilolin PDP 19 Tare Da Magoya Bayansu Dubu Hamsin Sun Koma APC A Kaduna

 

…”Muna yin kira ga Isa Ashiru Ya Hada Kai Da Gwamna Uba Sani A Ciyar Da Jihar Kaduna Gaba
Daga Imrana Andullahi
Isyaku Ishaya Duci, kansila ne mai wakiltar mazabar Yelwa da ke karamar hukumar Chikun a Jihar Kaduna da ya gabatar da jawabi a madadin sauran kansilolin ya tabbatarwa duniya cewa tuni suka canza sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC tare da dimbin magoya bayansu mutum sama da dubu Hamsin.
Honarabul Duci ya bayyana hakan ne a wajen wani taron gangamin da ya gudana a ofishin kamfe na Uba Sani da ke cikin garin Kaduna, inda ya ce kansilolin nan tare da magoya bayansu mutane sama da dubu Hamsin sun fito ne daga kananan hukumomi 23 na Jihar Kaduna, da kyakkyawar niyyar taimakawa Gwamna Uba Sani a samu nasara kwalliya ta biya kudin sabulu.
Honarabul Duci ya ce sun yanke wannan hukuncin ne na komawa jam’iyyar APC karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani saboda irin kokarinsa tare da jajircewarsa a wajen gudanar da al’amuran ci gaban Jihar.
Honarabul Duci ya kara da cewa bukatar Dara kasawa duk abin da yasa suka shiga harkokin siyasa shi ne domin samun ci gaba kuma a yanzu sun ga akwai haske a tare da tafiyar Gwamna Uba Sani don haka suka baro inda suke su bayar da tasu gudunmawar gare shi a ciyar da jihar Kaduna gaba.
 “Hakika a wannan lokacin da aka yi wannan taron gangamin a ofishin Kamfe na Uba Sani da kuma shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da Kashim Shatima, muna yin kira da babbar murya ga Isa Ashiru da ya zo ya hada hannu tare da Gwamnan Jihar Kaduna mai ci a halin yanzu domin a ciyar da Jihar Kaduna gaba”.

Da yake tofa albarkacin bakinsa a wajen taron gangamin wani Dattijo mai shekaru 75 Cif Dominic Aso – Ogi, cewa ya yi daman can akwai dadaddiyar alaka mai kyau tare da shi da Gwamna Uba Sani saboda an yi tafiya tare tun lokacin da Sanata Uba Sani ya yi takarar Sanata a  PDP a can shekarun baya don haka ya san Uba Sani ba tun yau ba.
Ya ce ” A matsayina na tsohon Soja da ke da shekaru 75 a halin yanzu a duniya ya yanke hukuncin shiga tafiyar Gwanna Uba Sani ne sakamakon irin kokarin da ya gani a zahiri daga Gwamna Uba Sani na rage kudin makaranta domin yara matasa su samu yin karatu da kuma irin yanzu yadda ya ga ana rabon kayan tallafin rage radadin cire tallafin man fetur da sauran kokari a kan irin yadda za a samu Jihar Kaduna ta ci gaba, hakan yasa na bar PDP a matsayina na tsohon Soja kuma jagoran mutanen da ke zaune a karamar hukumar Chikun da suka kasance kabilu masu bayar da dimbin kuri’a idan anzo zabe a koda yaushe”.
Muna yin kira ga Isa Ashiru da dukkan mutane manya da kanana da ke son ci gaban Jihar Kaduna da jama’ar ta da su bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga Gwamnatin Uba Sani da Gwamnatinsa a samu ciyar da Jiha gaba.
Wakilin mu ya ga irin dimbin jama’ar da suka halarci wajen taron da suka hada da Maza da Mata daga kananan hukumomi daban daban na Jihar

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.