Daga Imrana Abdullahi
Bayanin da muke samu daga Jihar Sakwato na cewa wadansu Likitocin Dabbobi na aikin ceton rayuwar wata kyanwa ta dan jarida Nasir Abbas Babi a garin Sakkwato.
Likitocin sun kebe kyanwar a wani wuri na asibiti don yin gwaje gwaje da karin ruwa bayan kyanwar ta fuskanci wata galabaita ta rashin cin abinci da ya haddasa mata shiga wannan mawuyacin yanayi.
Fatar mu dai Allah ya bayar da nasarar gudanar da aikin da ake yi.