Related Articles
Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana tsawaita dokar hana fita da kwanaki Talatin na Gaba, kuma ta mayar da kwana daya a matsayin ranar da jama’a za su sayi kayan abinci da Magunguna.
Sabanin irin kwanaki biyu na Talata da Laraba da a baya mutanen Jihar kaduna suka saba da su domin fita su sayi abinci da Magunguna, a yanzu Gwamnatin ta bayyana ranar Laraba kawai a matsayin ranar da mutane za su fita domin sayen kayan abinci da magunguna.
Bayanin hakan dai na kunshe ne a cikin wata takardar da mai ba Gwamnan kaduna shawara a kan harkokin yada labarai Muyiwa Adekeye, ya Sanya wa hannu.
Inda takardar ta ce bayan kwamitin kula da yadda al’amuran Covid 19 yake a fadin Jihar ya gano akwai yawaitar yaduwar lamarin a wasu Jihohi makwabta don haka aka kara daukar wannan matakin.
Gwamnan Kaduna Nasiru El- Rufa’i ya kara tsawon lokacin dokar hana fita da kwanaki 30 saboda irin yadda kwamitin kula da yanayin cutar korona a Jihar karkashin jagorancin Mataimakiyar Gwamna Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, kuma zai fara ne tun daga ranar 26 ha watan Afrilu 2020.
Takardar ta ci gaba da cewa lamarin shiga daga Jiha zuwa jiha da jama’a kan yi shi me ke kawo yaduwar cutar kuma tana yaduwa a wasu jihohi makwabta had da Abuja babban birnin tarayya don haka Gwamnatin kaduna ta ya dace a kara fadada tare da karfafa dokar.
A saboda haka ne aka duba yanayin kwanaki biyu da ake ba Jama’a su fita domin sayen kayan abinci da magunguna aka mayar da shi ranar Laraba kawai.
A game da kotun ta fi da gidanka da Gwamnatin Jihar kaduna ta kafa domin hukunta masu karya doka kuwa tuni aka bayar da izini cewa kotun za ta iya yin tara ko dauri ha wanda aka samu da matsalar karya dokar.
Kuma a game da batun yawan mutanen da za su halarci wurin Jana’izar rufe gawa idan an samu Rasuwa nan gababkadan za a fitar da tsarin yadda za a yi da kuma yawan mutanen da za su halarta ko yin aikin rufe gawar baki daya, kuma za a samu wannan ne daga ma’aikatar lafiya ta jiha.
Duba da irin yadda yanayin da ake ciki a yanzu ma’aikata da suke cikin Jihar kaduna suna yi wa Gwamnati aiki da ba su kai mutane dubu 100,000 ba da wadanda aka nada za su ci gaba da taimakawa sauran da a kalla sun kai mutane miliyan 10 a cikin jihar kaduna.
Gwamnatin Jihar kaduna ta bayar da umarnin cewa dukkan manyan wadanda aka nada da suka hada da kwamishinoni, manyan sakatarori, masu bayar da shawara da shugabannin bangarorin Gwamnati da kowanensu ya bayar da taimakon naira dubu dari biyar a watan Afrilu 2020
Sai kuma ga sauran watannin za su bayar da kashi 50 colin Albashinsu har sai wannan dokar zama a gida ta kare. Sai kuma sauran wadanda Gwamnati ta nada za su rika bayar da taimako domin a taimakawa wadanda ba su da karfi a cikin al’umma da ke Jihar.
Ma’aikacin gwamnati da yake karbar albashin dubu 67,000 zuwa sama zai bayar da tallafin kashi 25 colin dari na al albashinsa yayin da wannan lokaci na dokar hana fita. Babu wani ma daukacin da yake aiki zai kasa samun kasa da dubu 50,000 domin taimakawa rayuwarsa a cikin wannan hali na dokar hana fita.