Daga Imrana Abdullahi
An bayyana hukuncin da kotun koli ta yanke game da batun siyasa da zaben Jihar Zamfara a matsayin wata Ishara kasancewar mutane da dama ne suka taru a wuri guda amma kuma Allah madaukakin Sarki ya nuna ikonsa a kansu baki daya don haka dukkan yan siyasa a Jihar Zamfara da kasa baki daya lamarin ya zama Ishara a kansu.
Wani fitaccen dan siyasa daga karamar hukumar Talatar Mafara a Jihar Zamfara Alhaji Bashir Nafaru ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da wakilinmu ta kafar sadarwar “Whattsapp”, inda ya ci gaba da bayanin cewa dukkan yan siyasar Jihar Zamfara Allah ya tattara su duk da taron kangin nasu da suka yi a kansa ya Jefa su cikin kwandonsa don haka sai ayi hakuri zuwa wasu yan shekaru da fatan Allah ya tabbatar da abin da ya fi zama alkairi.
Nafaru, ya kuma yi kira ga Gwamnan Jihar Zamfara da kotu ta tabbatar mashi cewa ya duba Jihar Zamfara na halin da ake ciki na rashin tsaro duk da cewa kowa ya san ana iyakar kokarinsa amma ya kara kaimi sosai
Bashir Nafaru, ya kuma kara da fadakar da Gwamna Dauda Lawal da cewa ya kara kokari wajen zuwa ga Gwamnatin tarayya a amso dukkan abin da ya san hakki ne na Jihar Zamfara ya kwato domin azo a raba wa matasa kasancewar matasan na bukatar samun hanyoyin da za su samu abin yi, domin rashin abin yi ma na taimakawa wajen matsalar rashin tsaro don haka idan akwai abin yi za a samu sauki kwarai.
” Alhamdulillahi, ni da ba dan PDP ba amma duk da haka hukuncin kotun koli dole ne a ce wata Ishara ce daga Allah madaukakin Sarki, duk wani da yake ji da kansa a Jihar Zamfara cewa shi dan siyasa ce duk Allah ya tattara su a cikin kwando guda ya kawo wani mutum daya ya ce shi ne don haka muna goyon bayansa, Allah ka tabbatar mana da alkairi yasa a gama wannan mulkin nasa cikin kwanciyar hankali da lumana cikin hukuncin ubangiji.