Home / Labarai / Gwamna Dauda Lawal Ya Gayyaci Tsohon Gwamna Matawalle Domin Kaddamar Da Jami’an Tsaro
Hoton Gwamnan Jihar Zamafra Dauda Lawal daga Dama tare da Ministan tsaro Muhammad Bello Matawalle suna tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan kammala wani taro a garin Abuja babban birnin tarayyar Najeriya

Gwamna Dauda Lawal Ya Gayyaci Tsohon Gwamna Matawalle Domin Kaddamar Da Jami’an Tsaro

Daga Imrana Abdullahi
A kokarin Gwamnatin Jihar Zamfara karkashin jagorancin Dauda Lawal na ganin an kawo karshen matsalar tsaron duniya da lafiyar jama’a da ta addabi Jihar Jihar sanadiyyar hakan ake samun nakasu wajen Noma da gudanar da daukacin harkokin rayuwa baki daya, yasa Gwamnatin ta gayyaci ministan tsaro Muhammad Bello Matawalle domin kaddamar da jami’an tsaron da Jihar Zamfara ta horar da za a yi a ranar 31 ga watan Janairu, 2024.
Kamar yadda wata sanarwar da ta fito daga shugaban ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar ta sanar cewa Gwamna Dauda Lawal ya gayyaci ministan kasa a ma’aikatar tsaro Muhammad Bello Matawalle a matsayin bako na musamman.
Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya gayyaci tsohon Gwamna Muhammad Bello Matawalle ministan kasa a ma’aikatar tsaro domin ya kasance a matsayin baki na musamman a wajen taron da za a yi domin yaye jami’an tsaron al’umma da Gwamnatin Jihar ta horar da ake kiransu da (Askarawa), “Community Protection Guards”.
Kamar yadda wata sanarwar da ta fito daga shugaban kwamitin shirya taron Mouktar Lugga, taron da aka shirya za a yi shi ne a garin Gusau a ranar 31 ga watan Janairu, 2024, ana saran Gwamnoni shida ne za su halarci taron daga yankin Arewa maso Yamma, da kuma wakilai daga Gwamnatin tarayya da kuma jama’a a ciki da wajen Najeriya.
Hoton Gwamnan Jihar Zamafra Dauda Lawal daga Dama tare da Ministan tsaro Muhammad Bello Matawalle suna tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan kammala wani taro a garin Abuja babban birnin tarayyar Najeriya
Tun da dade wa dai Gwamna Dokta Dauda Lawal na yin kira yan siyasa da su ajiye batun bambancin siyasa a gefe kowa ya taho a hada hannu domin ciyar da Jihar gaba.
Ya ci gaba da bayanin cewa alkawarin da ya yi na cewa zai yi aiki tare da kowa kuma a bude ta hanyar aiwatar da aiki tare da gaskiya da Amana kamar yadda ya dauki alkawari tun a lokacin da ya yi rantsuwar kama aiki.
 Sauran wadanda aka gayyata sun hada da dukkan tsofaffin Gwamnonin jihar, tsofaffin Mataimakan Gwamnonin Jihar,yan majalisun tarayya da na Jiha masu ci da tsofaffi da kuma tsofaffin yan majalisar zartaswar Jihar, Sarakunan gargajiya da kuma dukkan shugabannin jam’iyyun da ke jihar.

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.