Home / Lafiya / An  Sake Samun Mutane 14 Da Suka Kamu Da Cutar Korona A Kaduna

An  Sake Samun Mutane 14 Da Suka Kamu Da Cutar Korona A Kaduna

Imrana Abdullahi
A wani taron da babban kakkarfan kwamitin da Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa domin kula da lamarin Korona bairus a Jihar, an tabbatar da bayar da rahoton karin mutane 14 da suka kamu da cutar.
Kamar yadda rahoton ya bayyana cewa an samu karin ne daga cikin almajiran da aka dawo da su Jihar daga Jihar Kano.
Kwamishiniyar lafiya ta Jihar ta bayyana wa kwamitin cewa za a iya samun karin wadansu masu dauke da cutar saboda a halin yanzu ana nan ana jiran zuwan sakamakon Gwajin da aka yi wa wasu daga cikinsu.
Kwamitin ya bayar da rahoton cewa almajiran da aka dawo da su suna nan a killace kuma basa cudanya da jama’a.
Kwamitin ya kuma bayar da bayanin cewa ya zuwa yanzu wadanda ke dauke da cutar sun kai mutane 41 kuma mafi yawancinsu sun kasance daga almajiran da aka dawo da su daga Kano ne.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun mai magana da yawun Gwamnan Jihar Muyiwa Adekeye.
Takardar ta ci gaba da yin kira ga jama’a da su hanzarta kai rahoton duk wani mutum da ya lallabo ya shigo cikin mutanen Jihar daga wani wuri domin a dauki matakin da ya dace.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.