Related Articles
…Za Mu Yi Hadin Gwiwa Da Duk Wanda Ke Bukata
Daga Imrana Abdullahi
Malam Hamza Yusuf, wani mai bincike ne kuma mai aikin bayar da horo a karkashin Da’awah Institute (DIN), da ke karkashin Islamic Education trust (IET), Minna Najeriya, ya bayyana cewa sun zo Jihar Kaduna ne domin su horas da mutane a kan abin da ake kira shari’a intelligence.
Wato aikin horas wa ne da ya kunshi abubuwa guda uku na ilimin addini wato na farko shi ne Usululfiqh, Qawa’idul fikihiyyah sai na uku maqasid al-Shari’ah
“Kuma duk lamarin ya samo asali ne bisa ga irin bambanci da kuma zafin ra’ayi na akidu da kuma na fahimta da ke cikin addini, saboda haka muna kyautata zaton idan har ilimin ya yadu za a samu fahimtar Juna domin za a samu dalili da kuma na kowace mazaba ne Malamai suka bi a kan hukunce hukunce na addinin musulunci”.
Hamza ya ci gaba da cewa “su kungiya ce ta addini sannan kuma ana yin wannan taro ne a dakin yin taro na Kungiyar Jama’atunnasarul Islam hedikwata Kaduna saboda haka an samo mahalarta wannan taron horaswar ne ta hanyar wasu manyan kungiyoyin addini, irinsu FOMWAN,JIBWIS,MSS,IMWON, Kungiyar Malaman Jihar Kaduna da Nisa’ussunna da dai sauransu ta hanyarsu ne muke yi wa maganar cewa muna bukatar mu shirya taron horswa sai kowa ya turo mana da wakilai su halarci taron horaswar.
Hamza Yusuf wanda ya kasance mai aikin gudanar da bincike ne ya kara da bayanin cewa kamar yadda sunan kungiyar ya bayyana da Islamic education trust Burin shi ne a zagaye duniya baki dayan ta ba kawai a garin Kaduna ba kawai, kuma a halin yanzu suna yin wani aiki da suke da Burin cimma a nan da shekarar dubu biyu da Talatin 2030 akwai yawan adadin mutanen da suke fatan yi wa horaswar nan a kan wannan aikin da muke yi a halin yanzu kuma za su yi ne a garuruwa da dama na Najeriya da duniya baki daya da ikon Allah”.
“Kamar dai yadda aka Sani cewa batun bambancin akida an samo shi ne tun lokacin rasuwar Manzon Allah SAW, sakamakon bambanci na fahimta da kuma hanyoyin da ake bi na zaro wasu hukunce hukuncen addini daman Burin wannan ba wai a tabbata a kan akida daya ba, shi ne dai a samu fahimtar Juna kuma a zauna lafiya shi ne ainihin Burin mu”.
A game da irin yadda za a samu kudin tafiyar da wannan gagarumin aikin a cikin addinin musulunci dole akwai batu na kudi, “amma dai duk da haka ana yin lamarin ne da taimakon Allah ana kuma bin wadansu hanyoyi a samu kudin yin wannan horaswar irin wannan da ake yi wa mutane a Kaduna, sannan ana yin sa ne ba tare da an karbi ko sisin kwabon kowa ba ga mahalarta horaswar ana dai yin hadin Gwiwa da wadansu kungiyoyi ne a shirya duk irin wannan taron
Sai Malam Hamza, ya yi kira ga duk wata kungiya da ke cikin garin Kaduna ko wajen ta da cewa a shirye suke ayi aikin hadin Gwiwa da duk kungiyar da take so a hada Gwiwa game da tabbatar da tafiyar aiki irin wannan da ikon Allah za a bayar da goyon baya dari bisa dari.