Home / Big News / An Cire Sakataren Hukumar Zakka, Da Mutane Biyu A Zamfara
Tambarin Mujallar Garkuwa kenan
Tambarin Mujallar Garkuwar Jama'a

An Cire Sakataren Hukumar Zakka, Da Mutane Biyu A Zamfara

 Imrana Abdullahi

Gwamnatin Jihar Zamfara ta sallamu Sakataren hukumar Zakka tare da wadansu mutane biyu daga wurin aikinsu

Su dai wadanda aka sallama aikin suna da mukamin Daraktoci ne a hukumar Zakka da wakafi ta Jihar, an kuma bayyana sallamar ne nan take.

Wannan matakin dai an dauke shi ne sakamakon taron da shugaban hukumar daraktocin Zakkar sula yi tare da mambobinsa a ranar Juma’a.

Da yake yi wa manema labarai jawabi a Gusau, shugaban hukumar, Furofesa Kabir Jabaka cewa ya yi mambobin hukumar ne suka yi koke cewa wadansu da duka ajiye aiki suna lalata kokarin aikin da hukumar Zakkar take yi na rabon Zakka da wakafi da ake ba mabukata a Jihar.

Kamar yadda Jabakan ya bayyana cewa lokacin aikin Sakataren hukumar tuni ya kare.

“A bisa dokar da ta kafa hukumar da kuma karfin dokar da aka ba su, mun cimma matsaya cewa daga yau sakataren hukumar tare da mutane biyu da suka kasance daraktoci mun sallame su daga aiki, kuma lokacin aikinsu a ofishinsu duk ya kare,” inji shi.

Saboda haka hukumar da nake wa jagoranci ni Futofesa Jabaka, min amince da nadin Aliyu Musa Marafa, da zai yi aiki a matsayin sakataren riko har sai an nada wanda zai zama sakataren hukumar.

Furofesa Jabaka, ya tabbatarwa da Gwamnatin Jihar cewa dukkansu tun daga kansa da mambobinsa baki daya suna aiki kan jiki kan karfi domin ganin an cimma nasara a hukumar Zakka da wakafi Jihar.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.