Home / Big News / Mutane Sun Dawo Daga Rakiyar Mu – Masari

Mutane Sun Dawo Daga Rakiyar Mu – Masari

Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bayar da shawara ga daukacin masu fada aji da su hanzarta daukar mataki ga ayyukan yan ta adda a duk fadin Kasar da su hanzarta yin abin da yakamat domin tabbatar da doka da oda a Jihar.

 

Gwamnan yana magana ne lokacin da ya karbi bakuncin Tawagar sojojin Nijeriya karkashin jagorancin babban jami’in soja mai kula da harkokin horaswa daga hedikwatar rundunar sojan Nijeriya Mejo Janar Leo Irabo, da suka kaiwa Gwamnan ziyara, inda Gwamnan ya tabbatar masu da cewa irin ayyukan da yan ta adda suke aiwatarwa abin bacin rai ne da suke haifar da damuwa don haka dole ne a yi maganin abin baki daya.

 

Masari ya ce, ” Ina cikin wani halin rashin tabbas sakamakon irin matsanancin halin rashin tabbas na tsaro da muke ciki musamman a Kauyuka da ke kan iyakoki da Dazuzzuka”.

 

“ A ranar Talatar da ta gabata ne babban jami’in yan sanda DPO na karamar hukumar Faskari aka kusa kashe shi. A yanzu yana can yana jinya a asibitin kashi sakamakon harbin bindiga guda biyu da aka yi masa ya samu rauni, ina fatar kuma Allah ya bashi sauki.

“ Haka kuma.lamarin ya faru a karamar hukumar Sabuwa inda aka kashe mutane biyar an kuma sace masu shanu. Sai kuma shugaban karamar hukumar Dan Musa da yazo daga Sabuwa da suka sace shi tare da Dansa duk an sace su.

 

” Sati biyu da suka gabata mun rasa akalla mutane 50 wanda a halin yanzu yan ta’ adda na gudanar da ayyukansu ne a kullum ba ko kakkautawa. Saboda haka mutane suna dawowa daga rakiyarmu don haka suke barazanar daukar makamai. ” ko a jiya wato yana maganar ranar ( Talatar da ta gabata, da misalin karfe uku na Dare sai da na dinga rokon shugabannin siyasar Faskari domin sun yi gangami za su fara fadaka da yan Ta adda.

 

“Hakika muna cikin wani mawuyacin hali na rashin tabbas. Kuma a halin yanzu ana Fuskantar lokacin Damina ne yana ta karatowa koda wadanda suke iya zuwa Gonakin su ma yanzu ba za su iya zuwa Gonakin ba saboda ayyukan yan Ta’adda da a yanzu suka mamaye wurare da dama a Jihar”, inji Masari yake gayawa tawagar sojoji

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.