Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya Karyata jita- jitar da ake yadawa wai cewa Tsohon Gwamna kuma ministan kasa a ma’aikatar tsaro Dokta Muhammad Bello Matawalle ya baya yan Ta’adda tallafi a Jihar Zamfara.
Ta yaya “shi da ba Gwamna ba zai bayar da tallafi ga yan bindiga?
“Muna yin kira ga Gwamna Dauda Lawal da ya rika yin ragowa ta kumbar Susa game da harkokin siyasarsa domin yin hakan ya na da matukar muhimmanci s matsayinsa na Gwamnan Jihar Zamfara”.
” A batu na gaskiya ban taba ganin wanda ake yi wa hassada ba kamar wannan bawan Allah domin hassadar ta baci ta kai inda ta kai, amma masu yin hakan sun mance cewar komai hassada Allah ne ke kare shi kuma abar masu yin hassada su yi ta yin hassadarsu domin kullum daukaka ake samu a game da wannan lamarin
Muna yin kira ga Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal da ya yi karatun tanatsu ya kuma zo ya zauna da minista Bello Matawalle domin Allah ya daukaka Jihar ya bayar da ministan tsaro ta yadda idan an tattauna za a yi maganin abin da ke damun jihar na rashin tsaro a zauna ayi magana Keke da Keke Suga yadda za su ciyar da jihar Zamfara gaba su kuma ga yadda za su hana yadda ake kashe karshen nan a Jihar Zamfara, ba wai ayi ta kazafi kala- kala ba.
” kuma duk wanda kaga kana yi masa irin wannan kazafin a kalla shekara daya ko biyu ai ya dace a saduda a bari ka san cewa Allah ya kare shi, kuma mune ainihin yaran ministan tsaro ya dace idan ma ya bayar da wani tallafi mune za mu Sani saboda haka ne muke cewa karya ne ba gaskiya bane batun bayar da duk wani tallafi ga yan bindiga domin hakan ba gaskiya bane domin ba wata magana mai kama da hakan”.
Ni Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, ina yin kira ga Gwamna Dokta Dauda Lawal da ya natsu ya san abin da ya kawo shi Gwamnan Jihar Zamfara ya san irin baiwar da Allah ya yi masa ta ya zama Gwamna kuma ya tuna alkawulan da ya yi wa mutane ya duba wahalhalun da ake ciki tare da kashe karshen jama’ar da ake ciki, ya san cewa ko ran dabba aka kashe sai Allah ya tambaye shi, ba kawai ya rika biyewa yan barandan siyasa ba da ke kokarin bashi shawarar siyasar da bata dace ba.