A ranar Asabar ne Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya gudanar da ziyarar gani da ido zuwa yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa a Ƙaramar Hukumar Gummi ta Jihar.
A makon da ya gabata ne mamakon ruwan sama ya haifar da ambaliya a wasu yankunan ƙaramar hukumar Gummi, inda ya lalata gidaje da dama.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta ce tawagar gwamna Lawal ta fara ne da gaisuwar ban girma ga fadar Mai Martaba Sarkin Gummi, Mai Shari’a Lawal Hassan.
A cewar sanarwar, gwamnan ya zagaya garin Gummi ne domin jajanta wa waɗanda ambaliyar ruwan ta shafa kafin ya wuce garin Gayari domin duba irin ɓarnar da ambaliyar ta yi.
Gwamna Lawal ya nuna matuƙar damuwa bayan duba irin ɓarnar da ambaliyar ta yi.
Ya ƙara da cewe, tuni tawagar injiniyoyi suka fara bincike a yankunan domin samun mafita mai ɗorewa.
“A yau, na zo ƙaramar hukumar Gummi ne domin yin jaje tare da gudanar da ziyarar gani da ido a yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa a makon jiya.
“Nan da nan bayan na samu labarin faruwar lamarin, sai na aika kwamishinoni biyu domin su kai ziyara kuma su jajanta wa al’ummomin da abin ya shafa.
“Bayan ziyarar mataimakin gwamna, na tura tawagar injiniyoyi domin su duba tare da sanin musabbabin ambaliyar ruwa.
“Yana da muhimmanci a lura cewa na ba da umarnin a fara aiki nan take don daƙile faruwar irin wannna matsalar a nan gaba.
“Ina so in yi amfani da wannan dama wajen sanar da ku cewa na bayar da gudunmawar buhunan abinci guda 10,000 da suka haɗa da shinkafa, masara, da gero, domin raba wa waɗanda ambaliyar ruwan ta shafa. Yanzu haka manyan motocin na kan hanyar Gummi domin a raba wa al’umma.
“Ni kuma a madadin gwamnatin jihar Zamfara, ina tallafa wa waɗanda abin ya shafa da Naira Miliyan 100. Bugu da ƙari, duk waɗanda abin ya shafa, za a raba musu filaye nesa da yankin da ke da haɗari domin su gina sabbin gidaje.”