Home / Uncategorized / GWAMNAN ZAMFARA YA KARƁI BAƘUNCIN SHUGABANNIN HUKUMAR RAYA YANKIN AREWA MASO YAMMA

GWAMNAN ZAMFARA YA KARƁI BAƘUNCIN SHUGABANNIN HUKUMAR RAYA YANKIN AREWA MASO YAMMA

 

 

 

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa ayyukan Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma sun yi daidai da ajandoji shida na ceton da gwamnatin sa ke da su.

 

 

Gwamnan ya karbi baƙuncin shugabannin Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma yayin da suka kai masa ziyarar ban-girma a zauren majalisa da ke gidan gwamnati a Gusau.

 

 

A shekarar da ta gabata ne shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya janye Ma’aikatar Raya Yankin Neja-Delta da Ma’aikatar Wasanni tare da Kafa Ma’aikatar Raya Yankin.

 

 

Ita dai sabuwar ma’aikatar da aka ƙirkƙiro ta na da hurumin kula da dukkan kwamitocin raya yankin, kamar Hukumar Raya Yankin Neja-Delta, da Hukumar Raya Arewa maso Yamma, da Hukumar Raya Kudu maso Yamma, da Hukumar Raya Yankin Arewa maso Gabas.

 

 

A nasa jawabin, gwamna Dauda Lawal ya yaba wa shugaba Tinubu kan kafa Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma.

 

 

“Lokacin dashugaban qasa, Bola Ahmad Tinubu, ya amince da ƙudurin dokar kafa Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma a shekarar da ta gabata, na yi imanin cewa ni ne wanda ya fi kowa farin ciki a ƙasar nan.

 

 

“Zamfara ta kasance a ƙasa a kusan dukkanin alƙaluman ci gaban ƙasar nan kuma tana fuskantar barazana da ƙalubale iri-iri. A bisa haka, na sake gode wa shugaban ƙasa bisa wannan abin a yaba masa na farfaɗo da yankin Arewa maso Yamma.”

 

 

Gwamna Lawal ya ce, ziyarar da mambobin hukumar suka kawo masa, wata dama ce mai kima ta yin haɗin gwiwa a cikin manufa ɗaya don ganin an samu ci gaba cikin sauri a jihar Zamfara, ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar ƙarancin abinci a yankin Arewa maso Yamma.

 

 

“Ayyukan ku sun yi daidai da ajandar ceto mai ƙunshe da abubuwa shida na gwamnatina: tsaro, aikin gona, ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa, da ƙarfafa tattalin arziki.

 

 

“Ina mai tabbatar muku da cewa za mu ci gaba da yin aiki tare da hukumar ku don ganin kun cika aikin da aka ɗora muku na samar da ci gaban jihar Zamfara da yankin Arewa maso Yamma, wanda shi ne babban shinge a ƙasar nan. Gwamnatina za ta ba ku duk tallafin da ku ke buƙata don sauƙaƙe ayyukanku a cikin jihar.

 

 

“A ƙarshe ina yi muku maraba da zuwa jihar Zamfara, a daidai lokacin da nake dakon ganin yadda za ku sauke nauyin da aka ɗora muku a jihar nan da nan kamar yadda aka tsara a cikin ajandar ku da suka haɗa da magance matsalar rashin tsaro da muhalli da dai sauransu. Na yi imanin cewa magance wasu matsalolin Zamfara, musamman rashin tsaro – waɗanda suka samo asali daga talauci, rashin aikin yi, da jahilci, da sauransu – zai haifar da zaman lafiya, kwanciyar hankali, da ci gaban yankin da ƙasar baki ɗaya.”

 

 

A farko dai, Shugaban Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma, Alhaji Lawan Isma’ila Abdullahi Yakawada, ya bayyana cewa Jihar Zamfara gida ce a gare shi, saboda kyakykyawan dangantakar da ke tsakaninsa da Gwamna da al’ummar Jihar.

 

 

“Mun zo nan ne don ziyarar ban girma don mu san juna. Na gaya wa abokan aikina cewa idan Zamfara ce, ya fi mana sauƙi fiye da Kaduna saboda ina jin kamar gida ne.

 

 

“Gwamna, wannan hukumar ’yarka ce; An yi sa’a, Arewa maso Yamma ita ce mafi girman shiyya a ƙasar nan. Ƙalubalen da muke fuskanta suna da yawa. Muna da shirin ci gaba na shekaru 10 na abin da shiyyar ke son cimmawa.”

About andiya

Check Also

PDP North West Zonal Youth Leader Commends Hon. Umar Yusuf Yabo

The People’s Democratic Party (PDP) North West zonal Youth Leader Alhaji Atiku Muhammad Yabo the …

Leave a Reply

Your email address will not be published.