Home / Uncategorized / Muna Kira Ga Jama’a Da Su Yi Rajista Da Jam’iiyar ADC A Zamfara – Bashir Nafaru

Muna Kira Ga Jama’a Da Su Yi Rajista Da Jam’iiyar ADC A Zamfara – Bashir Nafaru

Daga Imrana Abdullahi

Honarabul Bashir Nafaru Talatar Mafara tsohon Dan takarar majalisar wakilai ta tarayya a kananan hukumomin Talatar Mafara da Anka, ya bayyana sabuwar jam’iyyar ADC a matsayin hanya mafita ga daukacin jam’ar Jihar Zamfara.

“Muna yi wa Allah godiya da ya nuna mana wannan rana da muka ga sabuwar jam’iyyar ceton Najeriya da al’ummarta baki daya, wannan jam’iyya ta ADC da ake wa ganin karamar jam’iyya a can baya amma a yamzu ta na son zama ta daya ko ta biyu a Najeriya”.

Saboda haka Bashir Nafaru ya ce ya na yin kira ga iyaye, matasa da dattawa da su gaggauta yin rajista da wannan sabuwar jam’iyya ta ADC a kowace karamar hukuma mutane su gagguta yin rajista da ADC a matsayin yayan jam’iyya.

” Muna kara yi wa Allah godiya da a jihar Zamfara rikicin ta ya baci, amma a yanzu ga sabuwar tafiya da babu wani da zai ce shi ne Ubangida babu tsoho ba yaro babu wanda zai ce ni na kawo ka ko Ubamgidanka a cikin ADC ana gayyatar kowa ne ya zo ayi tafiya ta ci gaban al’umma muna kuma rokon Allah ya kafa mana ita a jihar Zamfara, idan kuma ka ba mu mulkin Allah ka rika mana mu samu damar kawar da matsalolin da muke gani a jihar Zamfara.

Duk da “ni ba Dan PDP ba ne ina APC ne amma a yanzu muna ganin ana neman a tsige Gwamna Dauda Lawal duk da irin namijin kokarin da yake yi wajen yi wa Jihar aikin ci gaban kowa baki daya, saboda adawa an tura masa batagari a cikin jam’iyyarsa da gidansa na mulki shi ne ake kokarin a cire shi, don haka irin wannan matsaloli idan Allah ya so ya nufe mu da kafa gwamnati zamu yi kokarin kawar da duk irin wadannan abubuwan baki daya”.

About andiya

Check Also

10,000 South East Pupils Get School Bags From Collins Onyeaji Foundation

    No fewer than 10,000 pupils in the South East Zone of Nigeria are …

Leave a Reply

Your email address will not be published.