Home / Big News / An Karrama Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar A Kaduna

An Karrama Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar A Kaduna

Daga Imrana Abdullahi
Sakamakon irin ayyukan alkairi da kokarin ciyar da addinin Musulunci da Musulmai ga a koda yaushe sun sa aka karrama Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar, Marafan Sakkwato da babbar lambar Karramawa.
Lamarin wannan gagarumar Karramawar dai ya faru ne a wajen babban taron Walimar yayen dalibai Maza da Mata da suka haddace Alkur’ani Mai girma da suka yi karatu a makarantar Nau’in Foundation Litahfizil Qur’an da ke kan Titin OHINOYI CLOSE OFF OHINOYI Unguwar Rimi GRA Kaduna.
A wajen wannan taron dai Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa Ƙauyukan Tsafe Abdulkarim Abdullahi wanda ya yi jawabi a madadin Sanata Yari ya kuma karbi lambar Karramawar da aka yi masa a madadinsa.
Sanata Abdul’aziz Yari ya ce a shaida maku cewa shima fa mahaddacin Kur’ani ne don haka a koda yaushe ya na farin ciki idan an samu mahaddatan Kur’ani a Najeriya da ko’ina a fadin duniya.
Tun da farko Katukan Tsafe, Abdullahi Abdulkarim, da yake gabatar da jawabinsa a matsayin wakilin Sanata Abdul’aziz Abubakar Yari, a wajen taron cewa ya yi  “a jiya ne wanda yake wakilta Alhaji Dokta Abubakar Yari,ya kira shi domin ya wakilce shi a nan, kuma ya ce lallai ina sanar da ku cewa shima mahaddacin alkur’ani ne don haka zai ci gaba da bayar da gudunmawarsa a wajen ciyar da wannan lamarin gaba.
“Ina duba nan da shekaru 36 muna yin karatu da mai girma Gwamna Sanata Uba Sani kuma ba wanda ya san za mu kai irin matsayin da muke a halin yanzu har ga shi ya na Gwamnan Jihar Kaduna a yanzu”, Inji shugaban ma’aikatan Abdul’aziz Yari.
A wajen wannan taron dai an samu yaye daliban da suka haddace Alkur’ani har guda 159 da suka kasance matasa Maza da Mata.

About andiya

Check Also

Sokoto Governor Commissions ₦12.6 Billion 8.1KM Yandaki–Shinkafi–Kofar Sauri Dual Carriageway

…We have constructed, rehabilitated, and upgraded over 200 kilometres of roads across Katsina State — …

Leave a Reply

Your email address will not be published.