Daga Imrana Abdullahi
A kokarinsa na ganin ya ci gaba da tallafawa dimbin al’umma Mata da Matasa Abdul’aziz Abubakar da ake yi wa lakabi da Kaka ya tabbatar wa da jama’a cewa zai ninka dukkan kokarin taimakon da yake yi wa al’umma idan ya samu damar zama dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar Kaduna ta Arewa a cikin jihar Kaduna.
Abdul’aziz Kaka Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen gagarumin taron da dimbin Mata suka taru a wurin dakin taro na Otal din Kwamand da ke Kaduna.
Abdul’aziz Kaka ya ce ko a wannan taron da akwai wadansu mutane guda hudu da ya yi wa hanyar shiga aikin Soja kuma a halin yanzu duk sun kammala horon su duk sun zama mutanen da kasa za ta yi alfahari da su.
“Ni ban yi niyyar tsayawa wannan takarar ba amma sakamakon irin Kiraye – Kirayen da jama’a ke yi sai muka yanke shawarar mu shiga takarar a dama da mu kuma muna ganin idan Allah ya so zamu lashe zaben fitar da dan takarar jam’iyyar APC da kuma zaben duka gari baki daya”.
“Muna yin kira ga daukacin jama’a da su ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon bayansu ga shugaba Bola Ahmed Tinubu, Gwamna Uba Sani da dukkan yan takarar da jam’iyyar APC za ta tsayar takarar kowace irin kujerar a kowane matakin”.
Da yake tofa albarkacin bakinsa babban daraktan yakin neman zaben Kaka, Alhaji Nasiru kira ya yi ga daukacin ya’yan APC da su ba su cikakken hadin kai da goyon baya ga yadda kwalliya za ta ci gaba da biyan kudin sabulu.
“Kowa ya san Kaka alkairi ne kuma muna fatan za mu lashe zabe ba tare da wata tangarda ba, ya kuma shaidawa jama’a cewa za a fitar da jerin sunayen yan kwamitin kamfen na tafiyar Abdul’aziz Abubakar Kaka na mutane dari da ashirin sai dai ya ce kowa na sa ne kuma duk sauran magoya baya su dauka suma mambobi ne a tafiyar”.
A wajen wannan taron dai an yi bayanin irin yadda Abdul’aziz Kaka ke taimakawa jama’a da suka hada da marayu da sauran jama’a da dama.
Jama’a da dama ne suka halarci wajen taron kaddamar da takarar Abdul’aziz Abubakar Kaka da suka hada harda wadansu mutane manyan ya’yan jam’iyyar APC da suka zo daga jihar Kano.
THESHIELD Garkuwa