Related Articles
Matane Ya Jajantawa Iyalan Marigayi Hassan Kolo
Mustapha Imrana Abdullahi
Kamar yadda wata sanarwa da ke dauke da sa hannun jami’in yada labarai a ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana cewa Alhaji Ahmed Ibrahim Matane ya bayyana matukar alhininsa tare da jajantawa Iyalan marigayi Alhaji Hassan Kolo da ya rasu bayan fama da yar gajeruwar rashin lafiya.
Marigayi Hassan Kolo ya taba zama jami’in yada labarai a ma’aikatar yada labarai ta Jiha, kuma ya zama mai magana da yawun Gwamnan mulkin soja na Jihar Neja, Kanar David Mark ( Mai ritaya) ya kuma zama Editan jaridar Newsline,manajan reshe na Bankin UBA, Darakta Janar na kungiyar Jema’a kuma ya zama Darakta Janar kuma Kantoma, gidan rediyon Jihar Neja da dai sauran mukamai da dama
Sakataren Gwamnatin na Neja ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa marigayin a ya Sanya shi a cikin Aljannatul Firdausi, ya kuma ba iyalan hakurin jure rashin da aka yi.