Home / Labarai / Wajibi Ne Matsa Su Yi Watsi Da Masu Ruruta Fitina – Lauya Aminu Abdrrashid

Wajibi Ne Matsa Su Yi Watsi Da Masu Ruruta Fitina – Lauya Aminu Abdrrashid

Wajibi Ne Matsa Su Yi Watsi Da Masu Ruruta Fitina – Lauya Aminu Abdrrashid
BARISTA Aminu Abdurrashid  Lauya ne mai zaman kansa da ke da ofishinsa a garin Kaduna ya yi wa manema labarai bayani a game da rikicin Kudancin kaduna da lamarin yaki ci yaki cinyewa duk da irin kokarin da Gwamnati ke yi, hakan tasa a matsayinsa na matashi ya fayyacewa jama’a yadda lamarin yake a mahangar doka ta yadda za a kawo karshen lamarin. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance da wakilinmu Mustapha Imrana Abdullahi ayi karatu lafiya.
Garkuwa : Shin yaya kake gani a game da wannan lamari na rikice rikicen yankin Kudancin Kaduna ganin cewa matasa ne ake yin amfani da su ana tayar da fitinar a mafi yawan lokuta.
Lauya Aminu : Da farko dai abin da yakamata a gane shi ne duk abin da za a dauki mataki na shari’a dole sai an kalle shi a shai’ance, sannan idan kana duban lamarin yadda aka samu lalacewar fahimta da rarrabuwar kai a tsakanin mutanen da suke a yankin Kudancin Kaduna dole sai an bashi kulawa da tsari irin na Lumana da sulhu a tsakani a tsakanin mutanen da ke zaune a wurin bisa matakin shari’a. An samu wadansu mutane da suke a wurin wajen shekaru 30 suna a wurin suna ta aiki irin na tunzura al’umma a kan tashin tashina da Barnar dukiya, wanda da yawa mutane ne da aka samesu da laifi ba wai ana tuhumarsu ba ne.
Babban matakin da yakamata a dauka shi ne duk wanda aka same shi da laifi a gurfanar da shi a gaban shari’a domin ayi masa hukunci bisa doka, saboda babu wani laifin da aka aikata da babu tanajinsa a tsarin doka kama daga farawa da su kisan kai, Kona Dukiya, batanci, cin zarafi da dai sauransu.
Kaga idan aka gurfanar da kowa ye ba tare da la’akari da inda mutum ya fito ba, ko idan an yi hukunci zai nuna cewa an goyi baya ko an yi wani fifiko, to in Allah ya yarda za a samu adalci domin ita shari’a ana bata siga ta makanta ne wato bata da Sani ba Sabo ba kuma fifiko a cikin shari’a hujjojin da aka gabatar a gabanta kwarara suke kai ga yanke hukunci.
Kuma yanke hukunci shike kai ga samar da lumana a cikin al’umma wanda yake ganin an bata masa ya ga cewa wanda ya bata masa bai ta fi haka nan sakai ba, in mutum ya aikata zai ga cewa ba za a bar shi haka kawai ba dole sai an samu irin wannan a farko kenan. Sannan na biyu maganar dai dai ta zamantakewa dole ne sai an cire siyasa baki daya daga cikin yadda ake tafiyar da al’amarin domin harkar siyasa ta shiga ciki duk Gwamnatocin baya da muka Baro hakika ta siyasantar da al’amarin domin yadda ake zuzuta cewa za a kaddamar da rahoton kaza za a tuhumi kaza, ai kullum cikin zuzutawa ake ba tare da an dauki matakin ba, wanda hakan ke ba da damar a fassara abin cewa ko akwai bangaranci ko bambanci na addini da sauransu.
Ita shari’a a tsanake ake yi kuma a cikin sirri wadansu abubuwan misali duk wanda aka samu an gurfanar da shi a gaban kotu kawai an tuhume shi ana ta shari’ar ba tare da an san me ake ciki ba amma a kazo aka ce za a yi yau gobe za a yi jibi  wannan shike haddasa ayi ta jita jita cewa saboda Gwamna ya fito daga wani bangare ne ko saboda yankin ba su bashi goyon baya ba da sauran irin wadannan abubuwa dole ne sai an cire irin hakan, a rika ruruta matakan da za a dauka kawai aga cewa ana daukar matakai.
Sa’Annan dole a samar da wani tsari matasa musamman su rabu da wadannan magabatan wanda wasu daga cikinsu wannan hanyar ita ce suke samu suna ci suna sha, ba tare da su matasan sun samu wani alfanu daga irin wannan aiki na matasan ba domin ba zaka ga Dattijai sun tare hanya suna kashe mutane ba, ba kuma zaka gansu suna Kone Kone ba duk wani abu na ta’addanci zaka ga matasa ke yi wani lokaci ma zaka ga ba wani ko sisin da ake ba su wani lokaci ma ko siyasar ma ba su da dama, ko ilimin kirki ba su da shi domin ko su matsan ma a yanzu da suke da ilimi ana amfani da su wajen gurbata tunanin mafi yawan matasan da ke cikin lunguna da sakon da ba su damar samun wayewar kai da ilimin ba wanda kuma su ake yin amfani da su wajen aikata barna, dole ne matasan da ke da ilimi sai sun taru isu isu an rage zazzafar kiyayya da maganganu na batanci da ake yi. Kwanan nan takaddamar da ta taso a cikin kungiyar Lauyoyi wasu lauyoyin da suka fito daga Kudancin Kaduna suka kalubalanci Gwamna a kan bashi dama ya gabatar da kasida a taron lauyoyi ya jawo wata zazzafar kiyayya domin yadda nake bin abubuwan a kafofin Sada zumunta musamman na Fezibuk zaka ga da wanda muke tunanin muna tare da su yan uwan mu lauyoyi daga wannan bangaren isu isu a tsakaninsu suna cin zarafin juna an gurbata tunani an lalata zamantakewa an ja bangaranci a kan yadda ake tafiyar da aikin lauya.
Kaga sai an soke irin wadannan ya zamanto duk wanda yake da ilimi ya zamanto takardar yake da shi a’a ya zamanto yana da basirar iya tafiyar da lamuran jama’a a aikace.
Kuma yana da kyau matasa daga bangarori daban daban mu zauna mu fahimci Juna duk wani abu da ya faru ya faru a can baya domin kada a mayar da hannun Agogo baya a tunkari me zai faru.
Misali a zauna a cikin garin Kaduna sai ace mutanen wani bangare ne na mutanen Zariya ne kawai ke da harkokin rayuwa na yau da gobe a Kaduna babu yadda za a ce a can Kudancin Kaduna kanshi ace kabilun da suke Kudancin Kaduna su za su tafiyar da rayuwar wannan bangaren dole sai an samu cudanya kamar yadda ake yi a kasuwanni kamar yadda ake yi a za a hadu a motar haya za a hadu a tasha, a samu amincewa da Juna hakan zai taimaka.
A cire zazzafar kiyayya da ke tsakani, kwatakwata matasa su daina sauraren musamman shugabannin da suka fito daga bangaren  Kudancin kaduna nan da bangaren SAKAMUDA din da bangaren SOKAPU din duk matasan mu su daina saurarensu su duba kawai su ga meye alkiblarsu, zaka ga wannan bangaren ya fito yana bayyana tarihi wannan ya riga wane zuwa duk mu cire shi a lissafi mu duba muga ya ma zamu yi a rayu a koma zaman da ake yi zaman da aka yi tun shekaru Talatin da aka yi zama na mutunci a can baya, wasu ma tun daga Katsina zaka ji mutum ya ce ya zauna a zankuwa za a iya nuna maka gidan da ya zauna ya yi koyarwa ko ya yi aiki Asibiti ko ya yi aikin Jirgin kasa kuma an yi zaman cudanya da auratayya da yan uwantaka wanda a wancan lokacin shi ya kawo irin ci gaban da aka samu , wannan shi ne kadai mafita ya warware rikicin. Sa’Annan Gwamnati ta daina maganar za ta aiwatar da kaza kawai ya zamanto cewa an gabatar da abin gaban kotuna an dauki matakai, wani lokaci koda yanke hukunci a kai amma akwai alkawari, a kan yanke hukunci amma a jingi ne aiwatar da shi a bisa alkawarin cewa mutum zai zama ya yi hali nagari a gaba wanda aka same shi da laifin  a gaba lallai za a tsaurara shi a gaba koda irin wannan matakan za a dauka to, za su kawo maslaha.

About andiya

Check Also

The Second Round Of Polio Commences On 20 to 23 APRIL 2024

  Parents and caregivers have been charged to ensure they make their children less than …

Leave a Reply

Your email address will not be published.