Home / News / Zamu Mayar Da Martanin Da Mutum Ba Zai Iya Mayarwa Ba – Dayuabu Kerawa

Zamu Mayar Da Martanin Da Mutum Ba Zai Iya Mayarwa Ba – Dayuabu Kerawa

Zamu Mayar Da Martanin Da Mutum Ba Zai Iya Mayarwa Ba – Dayuabu Kerawa

Mustapha Imrana Abdullahi
Alhaji Dayyabu Kerawa kansila ne mai wakiltar Mazabar Kerawa a karkashin jam’iyyar APC ya bayyana cewa nan gaba za su mayar da martanin da mutum ba zai iya mayar wa ba.

Kansila Dayyabu Kerawa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da kafar yada labarai ta rediyon Nagarta a cikin shirin Ance – Kace, inda ya ce akwai dimbin matsaloli a Karamar hukumar Igabi musamman a yadda ake tafiyar da jagorancin karamar hukumarsa.
” A dubi kamarsa ace wai ba shi da yafewa a mazabarsa duk da irin yadda ya yi kokarin yada manufa da kuma nemawa jam’iyyar APC jama’a lokacin zaben da ya gudana wanda kokarin gudunmawar ya haifar da samun nasarar APC a baki dayan karamar hukumar Igabi da kasa baki daya.
Ya ci gaba da cewa ” Na gayawa Gwamnan Kaduna baki da baki cewa ana kashe jam’iyyar APC a karamar hukumar Igabi, kuma kamar ni ace ba za a yi komai da ni ba da ya shafi matsaba ta, kuma koda batun Abubalar Mamadi ko babu ta yaya za a dubi kamarsa mai alfarma a ko’ina a kowace ma’aikata amma a rika yi masa yadda ake bukata a mazabarsa ta Kerawa don haka hakika zamu mayar da martanin da mutum ba zai iya mayarwa ba, wallahi”, kamar yadda ya ce.
Shugaban karamar hukumar Igabi a karkashin APC honarabul Jabir Kamis Rigasa na kokarin yi wa jama’a bayanin irin halin rashin kudin da suke ciki kamar yadda ya ce sakamakon biyan albashin Malaman Makarantar da suke biya da ya wuce naira miliyan dari da kuma sauran ayyukan raya kasa da ya aiwatar a fannoni daban daban.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.