Home / News / Gwamnonin Arewa Sun Ji Kunya ?

Gwamnonin Arewa Sun Ji Kunya ?

Gwamnonin Arewa Sun Ji Kunya ?

Mustapha Imrana Abdullahi

Wani dan jam’iyyar APC a Jihar Kaduna ya bayyana abin da Gwamnonin arewacin Nijeriya suka yi a matsayin abin kunya na rashin zuwa Sallar Jana’izar ta tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa.

Alhaji Yahaya Ji Sambo ne ya bayyana hakan a wajen wani taron manema labarai da yazo ta’aziyya a gidan marigayin da ke layin Turaki Ali cikin garin Kaduna.

Inda Ji Sambo ya ce “hakika abin da Gwamnonin arewacin Nijeriya suka yi na kin zuwa wajen Sallar zana’iza da kuma kin zuwa gaisuwar ta’aziyyar uban mutanen yankin Arewa musamman yan siyasa hakika abin kunya ne ga Jam’iyyar APC da daukacin manyan Arewa baki daya”.

Alhaji Yahaya Ji Sambo ya ci gaba da cewa a matsayinsa na dan jam’iyyar APC wannan irin hali da manyan yan siyasar Arewa suka nuna zai iya kawowa Jam’iyyar matsala tun a yanzu, saboda al’umma da dama irin abubuwan da suke fadi kenan cewa an yi watsi da marigayin.

Kuma hakika mutanen Arewa za su biyasu irin abin da suke yi na rashin zuwa su nuna Alhini a game da abin da ya faru saboda tun wadansu suna makarantar Firamare yake jagorantar aiki a wurare daban daban har ya zama Gwamnan Jihar Kaduna amma ya rasu sai ayi masa hakan.

About andiya

Check Also

Gwamnatin Hadin Kan Jama’a Na Haifar Mana Da Nasara – Gwamna Uba Sani

  …Nan da Sati biyu za a fara aikin garin Tudun biri Daga Imrana Abdullahi …

Leave a Reply

Your email address will not be published.