Home / Labarai / Babbar Kotun Tarayya Da Ke Abuja Ta Tura Sanata Ndume Gidan Yari

Babbar Kotun Tarayya Da Ke Abuja Ta Tura Sanata Ndume Gidan Yari

Babbar Kotun Tarayya Da Ke Abuja Ta Tura Sanata Ndume Gidan Yari

Mustapha Imrana Abdullahi
Babbar Kotun tarayya ta bayar da umarnin kai Sanata Ali Ndume gidan maza da ke Unguwar Kuje Abuja saboda kasawar sanatan ya kawo mutum da kotun ke nema.
Shi dai Sanata Ali Ndume ya tsayawa mutumin da ake tuhuma ne a kotun mai Suna Abdulrashees Maina inda sanatan ya tsaya masa kotun ta bayar da shi a hannun beli da yarjejeniyar duk lokacin da kotu ke nemansa in bai zo ba Sanata Ndume zai kawo shi.
Kasawar da Sanata Ali Ndume ya yi domin ya kawo tsohon shugaban rusasshen kwamitin fansho Abdulrasheed Maina, a gaban kotun, ya haifar da yanke wannan hukuncin.
Indai za a iya tunawa Ndume ya tsaya ne a matsayin mai tsayawa Mista Maina a game da karar da aka kai shi kan kudi naira sama da biliyan 2 da ake zargin an fitar da su daga Nijeriya.
Bayan bayar da shi Mista Maina a hannun beli, sai ya kasa bayyana a gaban kotu domin ci gaba da shari’ar tasa.
Da yake bayar da umarnin ranar Litinin, mai shari’a Okon Abang ya ce tun da ya kasa cika sharuddan da ya daukarwa kotu ya kawo Maina gabanta, don haka Sanata Ndume ya ta fi gidan Yari har sai ya cika dayan sharuddan da ya daukarwa kotu gida uku.
 Nan da nan aka wuce da Ndume daga dakin kotu bayan abin da kotu ta ce.
Zamu kawo maku ci gaban labarin nan gaba….

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.