Home / Big News / Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Wasu Mutane A Jami’ar ABU Zariya

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Wasu Mutane A Jami’ar ABU Zariya

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Wasu Mutane A Jami’ar ABU Zariya

 Imrana Abdullahi

 

Sanarwar da Daraktan Sashen Yada Labarai na jami’ar Ahmadu Bello Zaria Malam Auwalu Umar ya fitar a yammacin Litinin din na cewa a safiyar Litinin din da misalin karfe 12.50 na dare masu garkuwa da mutane suka shiga gidajen malaman jami’ar ABU da ke Samaru inda suka dauki wani ma’aikacin jami’ar da matarsa da kuma ‘yarsa.

Sanarwar wace muka samu  a shafin wayar da kan jama’a na jami’ar a dandalin Sada zumunta na  Facebook ta ce da ‘yan sanda suka bi sawun ‘yan bindigar sun yi nasarar kwato matar malamin da kuma ‘yarsa sai dai shi kuma sun gudu da shi. Jami’ar ABU din ta ce tuni ta sanar da hukumomin da suka dace.

About andiya

Check Also

An Yi Walimar Taya Soja Abdurrahman Abdullahi Shinkafi Murnar Zama 2nd Lieutenant A Kaduna

Daga Imrana Andullahi Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Mahmuda Aliyu Shinkafi, yi wa Allah godiya ya …

Leave a Reply

Your email address will not be published.