Home / Labarai / GWAMNAN BAUCHI YA RABA KEKE NAPEP DA MOTOCI

GWAMNAN BAUCHI YA RABA KEKE NAPEP DA MOTOCI

Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir na Jihar Bauchi ya sake raba keke NAPEP  guda dari 655 a karo na biyu da Motocin Sufuri 154 don inganta yanayin harkan Sufuri a jihar.
Gwamnan a lokacin da yake raba kayan a Bauchi, ya ce wannan raba Ababen hawa na daya’ daga cikin Shirin Gwamnatinsa Bauchi bayar da dama ga  al’umma dama na shiga wannan shiri don samun yalwatar arziki da dogaro da kai.
Ya ce dalilin kirkiro da wannan shiri da kuma aiwatar da shi shi ne muna da yakini da tsammanin cire jihar daga cikin Talauci.
” Ya na da mahimmanci a gareni kamar yadda aka zabe ni a Gwamna wadda nayi alkawarin zan muku aiki, Ina Kuma kara godiya wa Allah daya nuna mana wannan rana na Kaddamar da abubuwar da za su kara inganta tattalin arziki  ga dumbin wadanda  suka anfana da iyalansu da dukkan al’umma”.
” Hadakan wadannan Keke Napep da Motocin  Sufuri dazamu Bude a yanxu karakshin shirinnan da mukayi mata lakabi da  Kaura Economic Empowerment Program (KEEP 2020).
A lokacin da yake bude wadannan aikin guda biyu, Maigirma Gwamna Bala Muhammad yace Kashi na Uku dazaixo shine tallafi wa yan’kasuwa da masu Sana’ar hanu a jihar su zasu amfana batare da kudin’ ruwa ba wadda Shirin anzo matakin karshe na Kaddamar wa.
Yakara dacewa, karakshin Shirin, Zamu kaddamar da bada tallafi na kudi a hanu karakshin jagorancin kungiyoyin yan’ kasuwa da masu Sana’ar hanu ta hanun Ma’aikatan Kungiyoyi su zasu shirya yadda zamu bada  yadda za’ayi dakuma maida kudin’ a loakcin da yadace.
” Wannan Ma’aikatan yanzu hakq suna kan aiki  don tabbatar dacewa kudinda akabada yan’ kasuwa a wanchan Gwamnati andawo dashi don samun damar sake bada kudin saboda a sake bayarwa a yanzu wa wadanda zasu anfana da shirin.
Gwamnan yace  wadannan shirye shirye guda Uku da Gwamnatin jiha ta bullo dasu, xaibada dama wa aihin marasa aikinyi daga cikin matasa na samun damar inganta rayuwar su.
” Tunda Gwamnati baxata iya daukan kowa a matsayin Ma’aikatan Gwamnati ba, sun bude’ kofa wa masu kanfanoni masu xaman kansu dasuxo susaka hannun jarinsu kamar yadda muka bukacesu.
” Daga yau nasan hanyoyinmu zasu zamo busy sabida yawaitar  keke NAPEP yakaru dakuma. Tashoshin motocinmu don inganta harkan Sufuri .. “
Anasu jawabin daban daban, Kakakin Majalisar jihar Bauchi Rt Honourable Abubakar Y. Sulaiman da Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Bauchi, Hamza koshe Akuyam sun yaba wa Maigirma Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir na cika alkawarin dayadauka a lokacin kanfen musamman Kan inganta rayuwar al’umma.
Shima anasa jawabin, Kwamishinan Kungiyoyi da ci gaban Kananan Masana’antu, Alhaji Modibbo Ahmed bayyana jindadinsa da kuma Kara bada goyon bayan Ma’aikatan sa ga Maigirma Gwamna kan yunkurinsa na inganta rayuwar al’umma da rage radadin’Talauci.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.