Home / Ilimi / Masari Ta Karrama Yan Firamare Da Suka Wakilci Jihar Katsina

Masari Ta Karrama Yan Firamare Da Suka Wakilci Jihar Katsina

Gwamna Aminu Bello Masari ya yi kira ga iyaye da su rika juriyar sa ido da kula da tarbiyyar ‘ya’yan su mata, madadin su rika hana su zurfafa Ilimin su zuwa matakar gaba da Sakandare.
Alhaji Aminu Bello Masari ya yi wannan kiran ne a fadar Gwamnatin Jihar Katsina yayin da ya karbi bakuncin daliban makarantun Firamaren Gwamnati da suka wakilci jihar Katsina a gasar karatu da rubutu ta kasa da kuma gasar muhawara da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja.
Duk da cewa wadanda sukai gasar muhawara sun tsaya ne a matakin kusa da na karshe (quarter final), sun doke wakilan  jihohi da dama har da na babban birnin tarayya Abuja.
A daya bangaren kuwa, wadda ta wakilci jihar Katsina a gasar karatu da rubutu wadda daliba ce a Makarantar Firamaren Gwaji ta Gwamnati (Model Primary) da ke Faskari mai suna SUWAIBA HASSAN, ita ta lashe gasar, a inda tazo ta daya a jerin wadanda suka shiga gasar.
Wannan nasara da ta samu, tasa Jihar Katsina tazo ta daya a wannan gasa a jerin jihohin kasar  suka shiga.
Gwamna Masari ya jinjina ma wadannan dalibai musamman Suwaiba Hassan saboda wannan kokari da da dalibar ta yi.
Ya kuma mika godiyar Gwamnatin jiha ga Malaman wadannan yara da kuma shugabannin hukumomin ilimi a matakan kananan hukumomi da jiha.
A nasa jawabin, Shugaban hukumar Ilimin bai daya ta jiha (SUBEB) Alhaji Lawal Buhari, ya bayyana cewa wannan nasarori da ake ta samu, sakamako ne irin namijin kokarin da Gwamnatin Jiha keyi a bangaren ilimi.
Ya kuma yaba wa Gwamna Aminu Bello Masari saboda irin tsayuwar dakan da ya yi wajen an gyara harkar ilimi, musamman a wannan mataki na Firamare.
A ta bakin  Mahaifin Suwaiba, Malam Hassan, godiya ya yi cikin shauki, ga Gwamnatin Jiha, shuwagabannin hukumomin ilimi da kuma Malaman makarantun da suka zage damtse wajen ganin sun ba yaran kulawar da ta kamata wadda har ta kai su ga wannan mataki.
Daga  Hassan Mu’azu

About andiya

Check Also

APC RELOCATES TO NEW STATE HEADQUARTERS IN GUSAU, ZAMFARA

The Zamfara State chapter of the All Progressives Congress APC has today relocated to its …

Leave a Reply

Your email address will not be published.