Home / News / Farfesa Sule Bello Ne Shugaban PRP Ba Falalu Bello Ba – St Kamven Nannim  

Farfesa Sule Bello Ne Shugaban PRP Ba Falalu Bello Ba – St Kamven Nannim  

Farfesa Sule Bello Ne Shugaban PRP Ba Falalu Bello Ba – St Kamven Nannim
Mataimakin shugaban Jam’iyyar PRP reshen Jihar Kaduna st Kamven enoch Nannim ya bayyana Farfesa Sule Bello a matsayin shugaban jam’iyyar PRP na kasa  sabanin  yadda wadansu ke ikirarin cewa Falalu Bello ba.
” Ai mu a saninmu na yayan jam’iyyar PRP lokacin wa’adin shugabancin Falalu Bello tuni ya rigaya ya kare, kuma shi Falalu Bello ai ya  damar shugabanci ne lokacin da aka yi wani babban taron jam’iyyar PRP aka ce a bude kofa domin masu hannu da shuni su samu sukunin shiga a dama da su a cikin jam’iyyar shi yasa ya samu dama kuma hakan ya faru ne tun lokacin marigayi shugaban kwamitin Amintattun jam’iyyar Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa”.
Kasancewar Jam’iyyar PRP wadda take samun tagomashin Tururuwar mutane zuwa cikinta da a yau a Jihar Kaduna keda Ofisoshi a kananan hukumomi da mazabu ga kuma babban ofishinta na kasa ta yaya wasu za su rika ikirarin abin da ba haka ba?
“Kuma me yasa Falalu Bello ya tashi daga ainihin hedikwatar PRP ta kasa ya koma wani wuri idan ba ya san dama cewa shi ba shi ne shugabanta ba domin inda hukumar zabe ta kasa ta Sani da aka Sanya adireshin jam’iyya a wurin hukumar zabe shi ne ofishinmu na asali kuma shi ne har yanzu hedikwatar ba inda Falalu Bello ke ikirari ba”, Inji Kamven Nannim.
Ya kuma kira babbar murya cewa dukkan masu son shigowa jam’iyyar ana maraba da su manyansu da kananan domin bayanai na nuni cewa akwai dimbin jama’a suna nan suna shiga cikin PRP domin sun amince cewa ita kadai ce jam’iyya mai tsari da kudirin taimakon kasa da Talakawa baki daya.
“Koda takardar satifiket din jam’iyya na hannun wani marigayi ne shugaban kwamitin amintattun jam’iyyar PRP ya san abin da yasa ya bashi amma mu Farfesa Sule Bello ne muka Sani shugaba na kasa bayan haka ba mu san da kowa ba”, inji Kamven Nannim.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.