Related Articles
Ana Kokarin Haifar Da Rikicin Addini A Nijeriya – DSS
Mustapha Imrana Abdullahi
Hukumar tsaron farin kaya ta kasa (DSS) ta bayyana cewa akwai wani shirin da ya da ce ta ankarar da jama’a na kokarin haifar da fitina da sunan rikicin addini a kasa baki daya.
Hukumar ta ce wannan shirin da ake yi ana yi ne tare da samun goyon bayan wasu daga wajen Nijeriya. Kuma wuraren da ake kokarin haifar da wannan fitina sun hada da Jihohin Sakkwato,Kano,Kaduna,Filato, Ribas,Oyo,Legas da kuma wasu Jihohin yankin Kudu maso Gabs.
Bayanin hakan na kunshe a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar DSS ta kasa Dokta Peter Afunanya.
Daga cikin shirin da aka shirya shi ne a haddasa rikicin tsakanin addinai da kuma yin amfani da wasu mutane su kai hari a kan wuraren Ibada, a kan shugabannin addinai, kan wadansu muhimman mutane da kuma wuraren da gajiyayyu da marasa galihu suke.
A bisa haka ne muke bayar da shawara ga yan Nijeriya da su rika kulawa game da wannan lamarin su kuma gujewa dukkan wani kokarin tunzura jama’a da zai kai ga samun sabani da Juna.
Wannan hukumar tsaro na bayar da tabbacin cewa za su yi aiki kafada da kafada da sauran hukumomin tsaro domin ganin an ci gaba da samun kiyaye doka da oda.
Ana kuma yin hannunka mai Sanda ga masu kokarin aikata wannan mugun tsarin da su gujewa hakan domin samar da zaman lafiya da ci gaban kasa.
Ana kuma yin kira ga daukacin al’umma da su kai rahoton duk wani tsarin neman tashin hankali da ba su amince da shi ba ga hukumar tsaron da ke kusa da su domin daukar mataki.