Home / Labarai / Allah Ya Yi Wa Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Rasuwa

Allah Ya Yi Wa Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Rasuwa

Allah Ya Yi Wa Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Rasuwa

Imrana Abdullahi

 

Rahotannin da muke samu daga garin Karamar hukumar Makarfi da ke cikin Iihar Kaduna na cewa Allah ya yi wa tsohon shugaban majalisar dokokin Jihar Kaduna Alhaji Ahmed Hassan Jumare rasuwa.
Kafin rasuwarsa dai ya samu damar lashe zaben dan majalisar dokokin Jihar Kaduna inda har ya zama shugaban majalisar dokokin karkashin Jam’iyyar PDP.
Kamar yadda wakilinmu ya tuntubi wani na kusa da shi ya shaida mana cewa marigayin ya ya rasu ya bar mata biyu kuma yana da shekaru 61 a duniya ya kuma bar yaya sha Bakwai (17).
Kamar yadda muka samu sanarwa daga yan uwansa sun bayyana mana cewa za a yi Jana’izarsa a gobe idan Allah ya kaimu da safe.

About andiya

Check Also

Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Gwamnan Jihar Zamfara

APC SAK MATAWALLE GA ZAƁINMU SARKIN SHANUN SHINKAFI MUKE SO Daga Honarabul Abubakar Lauwali kaura …

Leave a Reply

Your email address will not be published.