Home / News / Shugaba Muhammadu Buhari Ya Kaddamar Da Yin Rajistar Yan Jam’iyyar APC

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Kaddamar Da Yin Rajistar Yan Jam’iyyar APC

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Kaddamar Da Yin Rajistar Yan Jam’iyyar APC
Mustapha Imrana Abdullahi
Shugaban tarayyar Nijeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da fara sabunta katin zama dan jam’iyyar APC a garin Daura.
Shugaba Muhammadu Buhari kenan sanye da fararen kaya a tsakiya yake nunawa jama’a katin zama dan jam’iyyar APC da ya sabunta
A lokacin da shugaban kasar ya je domin sabunta wannan katin nasa na dan jam’iyyar APC, Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, shugaban kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC tare da wadansu Gwamnonin na Jam’iyyar duk sun samu halartar wannan babban al’amari mai dimbin tarihi.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da Bashir Ya’u mai taimakawa Gwamna Masari a kan harkokin kafafen Sada zumunta na zamani a shiyyar Katsina.
Shi dai shugaban kasar ya samu halartar Rumfar Jefa kuri’a ta Babamgida ne mai lamba 001, a mazabar Sarkin Yara, cikin garin Daura a Jihar Katsina arewacin tarayyar Nijeriya, kuma da faruwar lamarin ya nuna a fili cewa an kaddamar da fara sabunta wannan rajistar kenan a kasa baki daya.
Daga cikin wadanda suka samu halartar wannan wurin kaddamar da sabunta katin dan jam’iyya sun hada da mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Mannir Yakubi, Sanatocin APC da yan majalisar wakilai na tarayya.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.