Related Articles
An Yi Wa Yan Dako Kyakkyawan Tsari A Kaduna
Mustapha Imrana Abdullahi
Barista Muhammad Sani Suleiman, shi ne sakataren hukumar kula da kasuwanni ta Jihar Kaduna ya bayyana cewa a kokarin Gwamnatin Jihar na ganin ta kare dukiyar jama’a yasa aka yi tsarin yi wa dukkan wani mai sana’ar yin Dakon kaya a Kwando ko Baro tsarin sama masa lamba domin a gane shi a koda yaushe.
Barista Sani Suleiman, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da kafar yada labarai ta KSMC inda yake yi wa jama’a bayanin irin tsare tsaren da Gwamnatin Jihar ke yi domin inganta kasuwanci.
Barista ya ci gaba da cewa Gwamnati ta yi la’akari da irin muhimmancin kare dukiyar duk wanda ya zo sayen kaya a cikin babbar kasuwar Kaduna yasa aka yi tsarin daukar sunaye da yi wa dukkan mai sana’ar Dako a cikin kasuwar Abubakar Gumi domin magance matsalar bacewar kayan jama’a ta hanyar dakon kaya.
“Zamu samarwa dukkan mai son yin sana’ar Dako a wannan kasuwa da rigunan aiki mai dauke da lambar kowane mutum, kuma hakan zai faru ne bayan da hukumar kasuwa ta dauki bayanai da wanda ya tsayawa mai son yin sana’ar Dako a kasuwar Abubakar Gumi duk domin a kara inganta kasuwar da kasuwanci tare da kyautatawa masu sayen kaya”.
Ya ci gaba da cewa da zarar mai sayen kaya ya sa yi kayansa ya ba dan Dako zai ga lambar wanda zai ba daukar kayansa a gaba da bayan rigarsa domin tantancewa da kuma saukin ganewa, sabanin irin yadda lamarin yake a da can baya.
“Muna son masu daukar dakon kaya a Kwanduna ko Baro ya zama duk an sansu ko wani abu ya faru za a yi saukin gane su”.
Barista ya ce an samar da wurin ajiyar motoci a gefen kasuwar Abubakar Gumi da zai ci motoci dari 470 a lokaci daya da za a rika ajiye motoci.
Kuma za a kaddamar da wannan wurin ajiye motoci a kasuwar Abubakar Gumi a sati mai zuwa, ” an inganta wannan wuri an Sanya na’urorin daukar hoton komai domin tabbatar da tsaro kuma dole duk Wanda ya ajiye motarsa za a bashi takardar sheda da ba zai fita da mota ba sai ya nuna domin shaida a kare dukiyar jama’a.
“Hatta masu yawon sayar da kaya a hannu a kasuwar Kaduna muna jiran su kawo sunayen mambobinmu domin hukumar kasuwa na da tsarin taimaka masu ta yadda za su samu yin kasuwancinsu cikin sauki, saboda haka muna nan muna jiran shugabanninsu su kawo sunayen.
Barista ya bayar da tabbacin cewa nan gaba kadan za a gina babbar kasuwar Dabbobi a hanyar zuwa filin Jirgin sama a cikin garin Kaduna, kuma a wannan wurin za a samar da mayankar Dabbobi ta zamani mai kyau da ingantaccen tsari.