Related Articles
Kungiyar Yarbawa Ta Tsame Kanta Daga Kiraye Kirayen A Raba Kasa
Mustapha Imrana Abdullahi
Shugabannin kungiyar jindadi da walwalar al’ummar Yarbawan Nijeriya baki daya da ke da babbar hedikwatarsu a garin Ibadan sun fito fili sun tsame kansu a kan kiraye kirayen da wani ya yi cewa al’ummar Yarbawa su tashi daga arewacin Nijeriya domin shi zai raba kasa.
Shugaban wannan kungiya ta jindadi da walwalar al’ummar Yarbawa ta kasa Abdulhakeem Adegoke ne tare da daukacin shugabanni da yayan kungiyar na kasa suka tsame kansu da irin wancan kiraye kirayen a lokacin da suke ganawa da manema labarai a Kaduna.
A taron manema labaran da suka yi a Kaduna sun tabbatarwa da duniya cewa babu wani ko wasu gungun yan siyasa ko masu kokarin tabbatar da son zuciyarsu da za su iya kawo wa Nijeriya cikas domin kawai wata bukata tasu ta biya.
Yayan kungiyar al’ummar ta Yarbawa sun ce babu ko shakka duk wannan lamari ne da ke tattare da siyasa kawai, ” duk wanda yake da wata nufaka da nufi irin na sisaya ya dace ya san inda zai samu yadda zai cimma burinsa amma ba ta hanyar haifarwa jama’a matsala ba domin kawai ya na neman jama’ar da zai yi siyasa da su”.
Shugabannin sun kuma yi kira ga yan uwa Yarbawa a duk inda suke a fadin Nijeriya baki daya da su yi zamansu a inda suke ba tare da matsawa kansu sai sun tashi daga wurin da suke ba, Nijeriya kasa daya ce al’umma daya da ta hada jama’a daban daban har da auratayya tsakanin al’umma Yarbawa, hausawa da Fulani don haka wani can zai zo rana tsaka ya lalata wannan tsarin da duk ci gaban da aka samu, hakika ba zai yuwuba.
Sun dai shaidawa manema labarai a Kaduna cewa su ne ainihin shugabannin kungiyar jindadi da walwalar al’ummar Yarbawa baki daya kuma shugabansu Abdulhakeem Adegoke ya taso ne daga garin Ibadan domin shaidawa al’ummar Yarbawa da duk daukacin yan Nijeriya cewa su zauna lafiya da junansu jada kowa ya tashi daga wurin da yake kuma a wannan taron manema labarai akwai shugaban kungiyar na yankin arewacin Nijeriya Nur’Deen Modu Ode, inda shima ya kara karfafa wa yayan kungiyar ta su Gwiwa da kuma muhimmancin zaman tare da Juna kamar yadda ake tun asali don haka ba ruwansu da duk wani kiraye kirayen a yaba kasa da wani ko wasu za su yi kira.