Gwamna Zulum Ya Bukaci A Sallami Ma’aikatan Lafiya 21 Da Aka Samu Da Takardun Bogi
…An Yi Wa Matattu Karin Girma Da Biyansu Albashi A Jihar Borno
Mustapha Imrana Abdullahi
Bayan samun wadansu ma’aikatan kula da lafiyar jama’a a Jihar Borno da takardun Bogi su 21 Gwamna Babagana Umara Zulum ya kuma tabbatar da an gano ma’aikatan Bogi 91 a Jihar.

Gwamna Babagan Umara Zulum tuni ya bayar da umarnin a dauki matakan ladaftarwa ga wadannan ma’aikata, bayan da kwamitin tantancewa ya gano ma’aikatan lafiya 21 wanda daga cikinsu akwai masu aikin jinya da suke aiki da takardun Bogi.
Kwamitin ya kuma gano wasu karin ma’aikatan daban har 91 da suka kasance duk na Bogi a cibiyoyin kula da lafiya a cikin Jihar.
Shugaban kwamitin binciken Dokta Josep Jatau ya bayyana hakan a ranar Litinin a Maiduguri, yayin da yake gabatar da rahotonsu ga Gwamna Zulum a karamin ofishin Gwamnan da ke sakatariyar ma’aikta ta Musa Usman.

Dokta Jatau ya bayyana cewa daga cikin wadanda suke aiki da takardun Bogi da akwai masu aikin Jinya, ma’aikatan lafiya da kuma masu aikin taimaka masu.
Shugaban kwamitin ya kuma yi bayanin cewa an gano mutane 91 da suka kasance ma’aikatan Bogi daga cikin jadawalin sunayen ma’aikatan lafiya a Jihar, wadanda ko dai sun ajiye aiki ko kuma sun bar aikin haka kawai amma kuma ana biyan Albashi Albashi sunansu.
Kwamitin ya gano cewa ana biyar kudin ma’aikatan Bogi miliyan 23 a kowane wata .
Kwamitin karkashin jagorancin Jatau, ya bayyana cewa sun gano wadanda suka mutu da wadanda suka tsere suka bar aikin da kuma matattu na cikin wadanda aka yi wa karin girma kwanan nan kuma ana biyan Albashi da sunansu a koda yaushe.
Bayan da kwamitin ya kammala gudanar da bincikensa sai suka bayar da shawarar a aikata abubuwa Goma sha uku (13) da za su taimaka a sake Sauya Fasalin hukumar da ke kula da asibitocin Jihar domin kwalliya ta biya kudin sabulu game da al’amuran lafiya ajiyar Borno.
Gwamna Zulum ya bayyana farincikinsa da nasarar kabala samu, amma kuma ya yi bakin cikin cewa wai za a samu ma’aikatan lafiya da takardun Bogi, duk da irin hadarin da aikin kula da lafiyar jama’a yake da shi ga dimbin al’umma sai ga wasu ba su da horon yin aikin kuma na wata takardar da ke nuna an yi karatun yin aikin, wannan abin bacin rai ne”, inji Zulum.

“Dukkan wanda aka samu yana aikin jinya da kula da lafiyar jama’a da takardun Bogi hakika zai iya kashe jama’a. Allah kawai ya san ko mutane nawa suka cutar ko kuma ma suka kashe baki daya. Don haka ba za mu bari wannan ya ta fi haka kawai ba , dole ne a hukunta dukkan wanda aka samu da laifi. Ba zan yi sako sako da dukkan wani al’amarin da ya shafi rayuwar jama’a da mutuwa ba. Abu mai muhimmanci kuma shi ne za mu dauki matakan hana faruwar irin wannan a nan gaba”, inji Zulum.