Home / Kasuwanci / Za’A Kafa Bankin Micro- Finance A Sakkwato, An Raba Biliyan 1 Matsayin Bashi Mai Sauki

Za’A Kafa Bankin Micro- Finance A Sakkwato, An Raba Biliyan 1 Matsayin Bashi Mai Sauki

Daga Imrana Kaduna
Gwamnatin Jihar Sakkwato karkashin jagorancin Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ta rabar da naira biliyan daya ga masu Tireda da masu sana’o’in hannu a duk fadin Jihar.
An dai yi wannan rabon kudin ne ga wadanda suka dace a wurin kaddamar da bankin Micro Finance na Jihar, an dai yi ne da nufin kara inganta harkokin rayuwar al’ummar Jihar ta yadda tattalin arzikin zai bunkasa a Jihar baki daya.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na mikawa wata mayar da ta amfana
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun Muhammad Bello mai ba Gwamnan Jihar Sakkwato shawara a kan harkokin yada labarai da kuma kafafen Labaran baki daya da aka rabawa manema labarai a ranar Juma’a a garin Sakkwato.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal wanda ya kaddamar da bankin Giginya Micro Finance a Sakkwato ya bayyana cewa za a rabawa mutanen da suka samu nasarar samun rancen mai sauki ne da za su rika biya a wata wata sannu a hankali cikin shekaru biyu domin wadansu su amfana”
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na gabatar da jawabi a wajen taron
Wannan bankin nabtalakawa na Giginya shi ne irinsa na farko da dan asalin Jihar da babban Bankin Nijeriya ya ba su lasisin gudanar da aiki.
Tambuwal ya kuma bayar da tabbacin cewa za a samu ci gaba a wannan fuskar domin za a yi kokarin samun kudi naira biliyan biyu daga Babban Bankin Nijeriya, “domin taimakawa masu sana’ar Tireda da masu kananan da matsakaitan sana’o’i ta yadda tattalin arzikin Jihar zai ci gaba da matsala tare da bunkasa”.
Ga hoton ofishin Giginya Micro Finance
Gwamnan kuma na yin wani shirin kara bunkasa wannan lamarin ta hanyar Sanya mutane yan Kwangida, masu ruwa da tsaki, Gwamnatin Jiha, bangarori da hukumomin gwamnati da masu zaman kansu tare da kungiyoyin gama kai suyi ajiya a wannan bankin”.
Kamar yadda ya ce Bankin zai kuma rika yin tsari irin na Bankin musulunci domin gudanar da harkar banki irin ta shari’ar Islama da aka amince ayi kamar Mudaraba,Murabaha,Salam, Ijara da Istisna.
Gwamnan ya kuma kara jadda cewa Gwamnatinsa a shirye take “ta ci gaba da taimakawa masu sana’ar Tireda da sana’o’in hannu domin samun saukin rayuwa ta hanyar bayar da bashi mara ruwa domin gudanar da sana’o’i daban daban.
Ya kuma yi alkawarin cewa nan bada komawa ba za a gudanar da tsare tsaren taimakawa masu sana’o’i daban daban.
A cikin jawabinsa Kwamishinan ma’aikatar kula da ciniki da masana’antu Alhaji Bashir Gidado godewa Gwamnatin Jihar ya yi bisa samar da wannan shirin yana cewa tsarin bayar da bashi zai taimakawa harkokin kasuwanci a Jihar.
Hoton mahalarta taron da aka yi a Sakkwato
Ya kara da cewa wannan bashin ba shi ne na farko ba da aka bayar ga masu sana’ar tireda ya bayyana cewa an bayar da naira miliyan dari biyar gare su a wani lokaci can baya
Shugaban Bankin, Alhaji Sambo Bashir, bayuana wannan tsarin ya yi da cewa kudiri ne na Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na fitar da marasa karfi da mata daga cikin kangin fatara da Talauci.
Wakilin Sarkin Musulmi Furofesa Sambo Wali Junaidu Wazirin Sakkwato, roko ya yi da cewa banda shirin na nufin kakkabe matsalar talauci a cikin al’umma ya kuma yi rokon cewa kashi Hamsin na wadanda za su amfana ya zamo mata ne.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.