Home / Labarai / Magance Matsalar Shaye Shaye Sai Kowa Ya Bayar Da Gudunmawarsa – Margaret

Magance Matsalar Shaye Shaye Sai Kowa Ya Bayar Da Gudunmawarsa – Margaret

Magance Matsalar Shaye Shaye Sai Kowa Ya Bayar Da Gudunmawarsa – Margaret

 

Mustapha Imrana Abdullahi
Shugabar gidauniyar da ke kokarin wayar wa da marasa Maza, Mata da sauran al’umma kai game da illar da ke tattare da shan miyagun kwayoyi Margaret K Julius, ta yi bayanin cewa dole sai kowa ya dauki himmar bayar da gudunmawarsa domin a samu magance matsalar a cikin al’umma.
Shugabar gidauniyar kulawa da Matasa da suka hada da Mata da Matasa Margaret K Julius, ta bayyana hakan ne lokacin da take yin jawabi a wajen taron wata wata da ake yi da aka yi wa lakabin aikin jarida domin samar da zaman lafiya da ake yi kowane wata a ofishin kungiyar tabbatar da dai- daito da kuma sasanci tare da zaman lafiya a tsakanin al’umma da ke Kaduna.
Margaret K Julius ta ce hakika akwai matsalar shaye shaye a tsakanin al’umma da ke bukatar kowa ya bayar da gudunmawarsa domin samar da maslaha a tsakanin jama’a su ga ne illar dauke tattare da miyagun kwayoyi da sauran abubuwan da ke da maye.
Ta ce “mafi akasari akwai rashin kulawar da ake yi wa masu shaye shaye wanda hakan na matukar haifarwa al’umma illa saboda masu yin wannan shaye shaye ko ta’ammali da miyagun kwayoyi duk zaune suke tare da jama’a don haka da zarar an yi watsi da su sai lamarin ya zama wani abu daban, amma ni sau da yawa na samu nasarar hana su yin shaye shaye kuma su na bari baki daya saboda haka idan ana matsayawa kusa da su za a samu nasarar hana su yin wannan ta’ammali da miyagun kwayoyi”.
Shugaba kuma wacce ta kirkiro da Gidauniyar kula da rayuwar Matasa da Mata da ke a jihar Kaduna wato Women and Youth Foundation Margaret K Julius, ta yaba wa Hukumar Kiwon Lafiya ta duniya (WHO), bisa sanya sunan Gidauniyar ta daga Nijeriya da za ta karbi lambar karramawa ta duniya ta shekarar  2021 kan kokarin da Gidauniyar ke yi na yin gangami da wayar da kan ‘yan Nijeriya  masu shan Taba Sigari  domin su bar yin ta’ammali da duk wata kwaya mai Sanya maye baki daya.
Gidauniyar  za ta karbi lambar  karramawar ta duniya, da ta fito daga gun Sakatare Janar na  Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya da kuma Sakatare Janar na Hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Da take ganawa da manema labarai a wajen taron  Shugaba Margaret K Julius, ta bayyana jin dadinta kan wannan karramarwar daga gun Tedros Adhanom Ghebreyesus.
A cewarta, “ A madadin daukacin tawagar Gidauniyar mu, ina mai mika godiya ga Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus, bisa zakulo kungiyar mu da kuma sanya ta a cikin jeren sauran kungiyoyi na duniya domin karramawa kan kokarin da muke ta yin gangami da wayar da kan masu dabi’ar shan Taba Sigari domin su daina don kare lafiyar su”.
Shugaba Margaret K Julius ta kara da cewa, “Muna masu godiya matuka kan sanya mu a cikin jerin wadanda za a karrama da lambar yabon ta shekarar 2021 kuma wannan karramawar, tamkar wani karin ci gaba ne ga Gidauniyar mu da kuma ‘ya’yan Gidauniyar baki daya saboda a yanzu za mu kara zumma”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.