Home / Labarai / Limamin Masallachin Haramayn Na Makka Ya Yabawa Gwamna Ganduje Ka Hidimtawa Musulunci

Limamin Masallachin Haramayn Na Makka Ya Yabawa Gwamna Ganduje Ka Hidimtawa Musulunci

… ..An nadawa Gwamna Alkyabbar girmamawa ‘yar asali 

Limami a Masallachin Haramayn na Birnin Makkah Mai Tsarki kuma shugaban Cibiyar Nazarin Larabci na Jami’ar Ummul Qura Farfesa Hassan Ibn AbdulHamid Al-Bukhari ya yabawa Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, bisa hidimtawa Musulunci da Gwamnan ke yi tare da gwamnatinsa.
Ya yi wannan jawabin ne lokacin da ya jagoranci tawagar wasu mashahuran malaman Jami’ar Ummul Qura, zuwa ga fadar gwamnatin Jihar Kano, yau Litinin, don sanar da Gwamnan abin da ya kawo su Jihar, bisa gayyatar Jami’ar Bayero ta Kano.
Bayanin hakan na cikin wata takardar sanarwar da ke dauke da sa hannun Abba Anwar Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano da ta ci gaba da cewa.
“Alhamdulillah tun mu na can mu na samun labaran aikhairin da gwamnatin ka ke yi wajen tallafawa cigaban Addinin Musulunci. Mun yi murna matuka da wannan labari da muke samu. Kuma mun zo mun gani ma da idonmu,” ya ce.
Ya kara yabawa yadda Gwamnan na Kano ya ke abubuwa saboda ci gaban al’ummarsa. Sa’annan nan ya tabbatar da cewa kullum a shirye su ke da su tallafawa Jihar ta Kano.
An bayyana cewar sun zo Kano ne bisa gayyatar jami’ar Bayero ta Kano, kan wata horaswa ta musamman da za su yi ga Alkalai da kuma daliban ilimi. Wannan ce kuma horaswa irin ta ta hudu da su ka yi a kasar nan.
A nasa jawabin Gwamna Ganduje ya bayyana yadda danganta ta jima tsakanin Jihar Kano da kasar Sa’udiyya tun shekaru da yawan gaske da su ka wuce.
Ya ce “…irin wannan dangantaka ce dadaddiya kuma mai inganci tsakaninmu, ta sa har Kasar ta Sa’udiyya ta bude wani ofishin jakadanci a nan Kano. Wanda duk wata alakarmu da wannan kasa mai Tsarki ta Sa’udiyya ta nan  ne mu ke farawa.”
“Alhamdulillah mu na da wani shirin na musamman dama da kasar Sa’udiyya wanda mu ke tura Malamai a na yi musu bita ta sati biyu ko uku. Daga baya bayan nan mun tura mata guda 100 domin su ma su amfana da irin wannan horaswa. Matan kuma Malamai ne na makarantun Islamiyya,” in ji Gwamnan.
Nan gaba kuma za a kara tura mutane wajen irin wannan horaswa. Kamar yadda ya bayyanawa wadannan manyan baki.
Cikin farinciki da walwala ya yi bayanin yadda Gidauniyarsa ta Ganduje Foundation ta ke yin kokarin gaske wajen hidimtawa Musulunci.
Kamar yadda ya ce “Wannan Gidauniya ni ne da kai na nake daukar nauyin dun aikace aikacen da a ke yi. An musuluntar da mutane sama da Dubu Ashirin (20,000) wadanda ba su da addini ko daya, sun shiga cikin da’irar Musulunci, Alhamdulillah. Kuma sama da shekaru 30 nake tare da wannan gidauniyar tawa.”

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.