Home / Labarai / Ba Gaskiya Ba Ne An Kaiwa Barikin Soji Na Jaji Hari Ba – Aruwan

Ba Gaskiya Ba Ne An Kaiwa Barikin Soji Na Jaji Hari Ba – Aruwan

Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Kaduna ta Karyata bayanan da wasu marasa kishi ke yadawa cewa wai an kai wa barikin soji da ke garin Jaji karamar hukumar hari.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne a cikin wata takardar sanarwar da ke dauke da sa hannun kwamishinan kula tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna Malam Samuel Aruwan, inda ya tabbatar da cewa wannan batu da wasu ke yadawa a kafafen yada labarai na yanar Gizo babu gaskiya a cikinsa ko kadan domin jami’an tsaron da ke aiki a wannan wuri sun tabbatarwa da Gwamnati cewa babu wani abu mai kama da hakan.
Kamar yadda aka rika yada labarin cewa wai a ranar Asabar 29 ga watan Mayu 2021 wasu mahara sun kaiwa barikin soji da ke Jaji hari lallai wannan ba gaskiya a cikin labarin.
A don haka Gwamnatin Jihar Kaduna ta Karyata wannan labarin da ake yadawa ta na mai cewa an yi ne domin karkatar da hankalin jama’a a kuma yada karya kawai.

About andiya

Check Also

Sokoto state government dethrones 15 traditional leaders, four others being investigated for various offences

  By S. Adamu, Sokoto Fifteen Sokoto traditional leaders have been dethroned by the Sokoto …

Leave a Reply

Your email address will not be published.