Related Articles
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Zamfara Dokta Bello Mohammed (Matawallen Maradun, Barden Hausa, Shattiman Sakkwato) ya sauke kwamishinoni da Sakataren Gwamnati da sauran wadanda aka nada a mukaman siyasa.
Wadanda lamarin ya shafa sun hada da Sakataren Gwamnatin Jihar,shugaban ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar da mataimakin shugaban ma’aikatan duk an sauke su daga mukaman da aka nada su nan take, sauran kuma sun hada da shugabannin hukumomi da ma’aikatun Gwamnati duk Gwamnan ya Rusa su.
Bayanin hakan na kunshe a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun babban mai ba Gwamnan shawara a kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a tare da sadarwa, Zailani Bappa da ta yi bayani kamar hakan.
Gwamna ya kuma bayar da umarni cewa wannan rushewar bai hada da wasu hukumomin Gwamnati da ke kunshe a cikin tsarin mulkin Nijeriya ba.
Duba da wannan umarnin dukkan kwamishinoni za su mika ragamar mulki ga manyan sakatarorin ma’aikatun da suke yi wa jagoranci, in ban da ma’aikatar kula da harkokin tsaro da harkokin cikin gida da ke karkashin DIG Mohammed Ibrahim Tsafe, su kuma shugabannin ma’aikatu da bangarorin Gwamnati Gwamnati su mika ragamar mulki ga Daraktan da ya fi kowa girman mukami sai kuma shugaban ma’aikatan Jihar zai kula da ayyukan ofishin sakataren Gwamnatin jihar da aka rushe.