Related Articles
Mustapha Imrana Abdullahi
Kwamishinan ma’aikatar harkokin addini na Jihar Kano Muhammad Tahar Adamu, ya bayyana cewa an Sanya ranar Asabar 10 ga wannan watan da muke ciki ta zama ranar da za a yi mukabala tsakanin Malaman addinin musulunci da kuma Abduljabbar Muhammad Nasiru Kabara, bisa zargin da ake yi masa na yin laifin batanci ga musulmi da addininsu Bali daya.
Muhammad Tahar Adamu ya bayyana cewa tuni ya je da kansa ya kaiwa kowa ne bangare takardar sanarwar taron mukabalar da za a yi a ranar Asabar 10 ga wannan wata da muke ciki a hukumar shari’a ta Jihar Kano da safe a kuma kammala da Yamma in Allah ya kai mu.
Ya ci gaba da bayanin cewa Gwamnati ta yi tanajin samar da tsaro ta yadda dukkan wanda yazo wurin zai koma gidansa lafiya.
Sai dai ya ce wadanda aka amincewa ne kawai za su yi magana a wurin taron don haka ba a yarda kowa ya ce uffan ba lokacin da ake gudanar da taron, saboda haka duk wanda bashi a cikin wadanda za su yi magana za su kasance yan kallo ne kawai.