Abdullahi Sheme
An yi Kira ga Gwamnatin tarayya da ta samar da ingantaccen tsaro a yankunan karkara domin inganta noma a kasar nan Wannan kiran ya fito ne daga bakin Wata Babbar Manomiya Hajiya Ramatu Usman Funtuwa a lokacin da take raba ragowar takin zamani tirela 2 na yuriya ga kungiyoyin manoma 52 da ke shiyyar funtuwa a jahar katsina.
Hajiya Ramatu Usman itace shugabar kungiyar Magpaman ta kasa reshen jahar katsina tace ta dauki tsawon shekaru da ya wa tana gudanar da harkar noma ita da kanta ta kirkiro da wannan shirin na kungiyar bani inabaka watau Anchor Barrower tace tun a cikin watan Afirilu watan 4 na wannan shekarar da muke ciki ta rabawa kungiyar manoma 52 mai mambobi sama da mutum 1552 da ingantattun irin shukawa na masara da maganin feshin kashe hakii a kananan hukumomi 11 dake yankin shiyyar funtuwa da bayar da buhunan takin NPK har tirela 6.
Hajiya Ramatu taci gaba da cewar kananan hukumomin da suka sami shiga shirin bani inabaka watau Anchor Barrower sune karamar hukumar funtuwa da Musawa da Matazu da Malumfashi da Kafur da Bakori da Danja da Sabuwa da Dandume da Kankara da karamar hukumar Faskari Hajiya Ramatu wadda take noma masara sama da buhu 2000 a gona kinta hekta 150 tayi kira ga dukkan matasan yankin da su rungumi sana’ar noma suma mata su tashi tsaye wajen gudanar da noma domin ba wai maza kadai ke noma ba sannan tayi kira ga Gwamnatin Tarayya a karkashin jagorancin Shugaban kasa Alhaji Muhammadu Buhari ya kara daukar mataki wajen kawo karshen ta’addancin daya addabi al’ummar yankin tace idan Gwamnatin bata dauki mataki da wuri ba noma zai gagari yi a yankin Arewa musamman a jahohin. Katsina da Kaduna da Zamfara da Sakkwato da jahar Neja ta roki Manoman yankin da suyi amfani da ragowar takin da zasu karba tirela 2 na yuriya kuma su sani bashi ne da zarar sun kammala kwashe amfanin gomar su su maido da bashin da a ka basu domin haka yarjejeniyar take ta yabawa Gwamnatin tarayya wajen inganta harkar noma sannan tayi kira ga dukkan al’ummar jahar katsina dasu tashi tsaye wajen gudanar da addi’o’i domin samun zaman lafiya a fadin jahar dama kasa baki daya ta godema Gwamnan jahar Alhaji Aminu Bello masari yadda yake gudanar da manyan aiyuka a fadin jahar Shuwagabanin kungiyoyin manoman na kananan hukumomin 11 na shiyyar sun yabawa shugabartasu Hajiya Ramatu wajen kokarinta da jajircewar da take dashi wajen taimakon Kananan Manoman yankin kuma sun bata tabbacin maido da bashin da zarar lokaci yayi a jawabinta na godiya Hajiya Rabi Aminu wadda ta wakilci sauran matan Manoman yankin da suka amfana da shirin ta yabawa shugabar wajen kwazonta da jawo mata shiga harkar noma