Home / Labarai / Yan bindiga Sun Kashe Dan Sanata Bala Na’allah

Yan bindiga Sun Kashe Dan Sanata Bala Na’allah

Mustapha Imrana Abdullahi
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta ce wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe Kyaftin Abdulkarin Bala Ibn Na’allah babban ɗa ga Sanatan.
Cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ASP Muhammad Jalige, ya tabbatar da mutuwar Kyaftin din sojin.
” Wasu ne da ake zargin ‘yan bindiga ne suka shiga gidan Abdulkarim da unguwar Malali a yammacin ranar Lahadi suka kashe shi. Bayan sun kashe shi sun tafi da motarsa guda, amma lokacin da suka je gidan matarsa ba ta nan, dama ba su da ko ɗa, in ji ASP Jalige..
Wasu ne da ake zargin ‘yan bindiga ne suka shiga gidan Abdulkarim da unguwar Malali a yammacin ranar Lahadi suka kashe shi.
 Bayan sun kashe shi sun tafi da motarsa guda, amma lokacin da suka je gidan matarsa ba ta nan, dama ba su da ko ɗa, in ji ASP Jalige..
Rahotanni daga Najeriya na bayyana Abdulkarim a matsayin Kyaftin din sojin Najeriya, sai dai da BBC ta tambayi ASP Jalige kan matsayin marigayin sai ya ce “gaskiya ban san matsayinsa ko aikin da yake ba, amma har yanzu muna tattara bayanai kan wannan lamari.”
Duk da cewa ‘yan sanda sun ce ba su kammala bincilke kan batun ba, amma rahotanni na cewa za ayi jana’izarsa a makabartar anguwar sarki a Jihar ta Kaduna.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.