An nada Aminu Ado sabon sarkin Kano.
Mustapha Imrana Abdullahi
Sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a gidan gwamnati ranar Litinin, jim kadan bayan sauke Sarki Sanusi II.
Gabanin nadin nasa shi ne sarkin sabuwar masarautar Bichi da Gwamna Ganduje ya kirkira a shekarar 2019.
Aminu Ado Bayero wanda da ne ga marigayi Sarki Ado ya zama sarki na 15 a jerin Sarakunan Fulani na Kano.