Home / News / NA YI AIKIN BILIYOYIN NAIRA A MAZABA TA – IBRAHIM MUSTAPHA ALIYU

NA YI AIKIN BILIYOYIN NAIRA A MAZABA TA – IBRAHIM MUSTAPHA ALIYU

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
HONARABUL Ibrahim Mustapha Aliyu dan majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Raba da Wurno daga Jihar Sakkwato wanda ya kasance mataimakin shugaban kwamitin tsara birane da yan kuna a majalisar wakilai ta kasa ya bayyana cewa ya yi wa mazabarsa aikin raya kasa da kudin suka kai sama da naira biliyan daya.
Honarabul Ibrahim Mustapha Aliyu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja.
Honarabul Ibrahim Mustapha ya ce duk da cewa aikin dan majalisa shi ne yin doka da kuma zuwa aikin zagayen Sanya idanu domin ganin aikin da aka yi da kudin da aka ware a don yin aikin wanda majalisa ta amince da su.
“Saboda irin yadda na san hakkin da ya rataye a wuta na ban yi kasa a Gwiwa ba, sai da na yi kokarin sama wa mazaba ta ayyukan raya kasa, koda yake ni a wuri na abu ne da har ma na mance da shi misali daga titin  marabar Raba zuwa marabar Bakura da aka yi shi a tsawon shekaru Talatin da hudu da suka gabata kuma ya lalace kwarai ga kuma allumar wannan wuri na cikin matsalar rashin hanya, wato matsalar samun sahihiyar hanyar daukar kayansu musamman na amfanin Gona ya zama masu wahala kwarai don haka na ga cewa lokaci ya yi da zan rungumi wannan lamarin aikin hanya sai kawai na gabatar da kudiri a gaban majalisar wakilai ta kasa kan a gina wannan hanyar kuma na yi ta bibiyar lamarin, ina farin cikin shaida maku cewa a yanzu an kusa kammala aikin wannan hanya abin da ya rage kawai bai fi yan gyare gyare ba sai a kammala ainihin gundarin aikin a shekarar 2023. Ina jin a halin yanzu aikin zai kai kudi daga miliyan dari Takwas zuwa naira biliyan daya da Digo biyu (1.2b) kuma tsawon hanyar ya kai kilomita Tamanin da daya (81).
“Na kuma samu nasarar samun aikin gyaran matsalar zai zayar kasa a wurare shida (6) Wurno, Raba, Marnuna, Rara,Gidan Buwai da garin Achida da aikin zai lashe kudi sama da biliyan biyar da miliyan dari shida (560b) ayyukan kuma sun hada da gyaran wuraren hanyoyi gyaran magudanan ruwa da wuraren da suka zai zaye har ma da kwalbatai da duk wuraren da ke bukatar ayi gyara sakamakon matsalar da aka samu ta zai zayawar kasa. Sai kuma a bangaren batun ilimi mun samu nasarar samun aikin gina Ajujuwan makarantun Firamare da a halin yanzu an samu nasarar gina sama da guda Bakwai mun kuma samu nasarar yin aikin tituna a Rara, Yar tsakuwa, Gidan Bango kuma mun gyara fadar Hakimi.
Kuma mun yi aiki sosai a bangaren batun rage radadin talauci mun samu raba wa jama’a Babura, Kekunan Dinki, Injunan Saka domin karfafa wa mata su dogara da kawunansu.
Sai kuma bayar da Injunan banruwa ga manoma kasancewar mazabata kusan duk manoma ne don haka abin da kawai zaka yi shi ne ka taimaka masu su samu yin aikin Noma mai yawa.
Akwai kuma ayyukan hadin Gwiwa na mazabu a bangaren makarantu da suka hada da taimakawa dalibai
Irin kudin tallafin karatun da muke ba dalibai da suke karatu a manyan makarantu da kuma bayar da tallafi domin yin jarabawar JAMB tare da yi masu aikin horaswa a kan yadda za su samu damar rubuta jarabawar cikin sauki bayan sun samu makamar aiki.
Da akwai kuma wadansu shirye shirye da dama suk domin inganta rayuwar mutanen mazabar da nake yi wa wakilci a majalisa. Sai kuma aikin samar da wutar lantarki daga Tofa zuwa Bomawa masaga da ya hada a kalla manya manyan garuruwa shida da suka hada da raban maba, Gawakuke, Gidan almajiri, burmawar masaga,burmawar liman da gidan Doka ana nan ana gudanar da aikin da akwai kuma wani aikin samar da wutar lantarki a Tunga da tuni har an kammala aikin da dai wasu da yawa da ba zan iya tunawa ba domin hakika mun yi aiki sosai da yawa don haka muke yin godiya ga Allah da ya ba mu damar aiwatar da aikin.
Kasancewar yankin mazabarka na daga cikin wuraren da ke fama da matsalar yan Ta’adda da sace sacen mutane, a matsayinka na dan majalisa shin wane kira kake da shi game da hakan?
Sai dan majalisa Ibrahim Mustapha Aliyu, ya ce ni hakika bayani na a nan shi ne a kula domin abin nan ya yi yawa domin akwai wani lokacin da yan bindigar nan sula je garin Raba suka sace wani jami’in kula da kiwon lafiya kuma suka sace Dabbobi da yawa da akwai kuma irin wadannan matsalolin da ake samu a kusan kullum.
Wato matsalar shi ne mafi yawan abubuwan da muke aiwatarwa da ci gaban jama’a za su iya samun matsala sakamakon irin wannan, amma duk da hakan ina bayar da tabbacin cewa mu na daukar kwararan matakai na kwarai, wasu daga cikin masu wannan aikin an san su da wadanda suke hada kai da su don haka muke rokonsu domin Allah su canza zuciyarsu saboda su Sani cewa za su yi wa Allah bayanin komai a ranar gobe.
Kuma a matsayinsu na mutane ya dace ya zama su na da tunanin dan Adam ta yadda suke Sanya rayuwar jama’a cikin matsala su na kashewa, Fade, satar dukiyar jama’a da sauran ayyukan ta’addanci da dama ta yaya za su yi Karko su na aikata irin wannan aikin Ta’adda da suka zagaye kawunansu da shi, duk da cewa kowa ya san kwanakinsa kididdigaggu ne don haka dole ne wata rana za ta zo saboda haka muke kiransu domin Allah su canza halin su a samu zaman lafiya.
Ko akwai gamsuwa game da matakan da ake dauka? Sai dan majalisar mai wakiltar Wurno da Raba ya ci gaba da bayanin cewa ba zai ce ya amince ba kuma babu wata hujjar da zai ce A’a, na dai san jami’an tsaron na yin iya bakin kokarinsu domin yin abin da ya dace sai dai kawai ana samun kalubale kawai.
Duk da batun tattalin arzikin da ake fuskanta mun san shugaban kasa na yin iya bakin kokarinsa kuma ya ba harkar tsaro kulawa sosai, amma dai a kara kokarin sosai.
Ko a kwanan nan sai da na gabatar da wani kudiri a gaban majalisa game da batun yan ta’addan din nan wanda sakamakon hakan duk majalisar ta amince cewa shugaban sojojin Najeriya ya hanzarta samar da sojoji da kayan aiki zuwa Raba da Wurno da kuma samar da sansanin sojoji a Gandi da mahadar Rara zuww Bulla da Wurno.
Sai kuma shugaban na sojoji ya samar da wurin da sojan za su rika yin aiki daga Munki saboda a baki dayan yankin Sakkwato ta Arewa babu wani san sanin sojoji da hakan ina bayar da tabbacin cewa an samu kai wa jama’a daukin gaggawa ga duk inda ake bukatar hakan a samu ceton rayuka da dukiyar jama’a.
Kuma tun daga kan mai bayar da shawara a kan harkar tsaro, babban sifeton yan Sanda, jami’an tsaron DSS da dukkan hukumomin tsaro mun yi kira a gare su da su kai jami’ansu wadannan wuraren domin a samu tattara bayanan sirri cikin sauki a samar da tsaron lafiya da dukiyar jama’a

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.