Mustapha Abdullahi
Sabon zababben shugaban Jam’iyyar PDP na karamar hukumar Bakori a Jihar Katsina Honarabul Abubakar Tsoho ya bayyana kudirinsa na kare mutuncin jama’a ta hanyar Nemo wa kowa yancinsa a koda yaushe a matsayin abin da zai Sanya a gaba lokacin shugabancin nasa.
Abubakar Tsoho ya bayyana hakan ne a cikin wata takardar da ya aikewa manema labarai. Inda ya ce hakika ya lashi takobin kiyaye mutuncin yayan jam’iyyar tare da sauran al’umma baki daya da ke kowane sako da lungu na karamar hukumar Bakori.
Tsoho ya ci gaba da cewa kasancewar jam’iyyar PDP jam’iyyar ce ta Afirka da duniya baki daya ta kasance tana da tsare tsare da tanaje tanaje da dukkan dokokin da ake bukata don haka za a kiyaye su a lokacin shugabancinsa a karamar hukumar Bakori.
Ya kuma yi kira ga daukacin jama’a su kara jaddada goyon bayansu ga jam’iyyar PDP kasancewar ta taka mihimmiyar rawar a gani a fada a fadin Jihar Katsina baki daya don haka ya dace a sakawa PDP da irin ayyukan rays kasar da ta gudanar a tsawon shekarun da ta yi mulki a Jihar katsina.
“Indai ana son ci gaba da samun ayyukan taya kasa a kowane sako da lungu na Jihar Katsina baki daya, da ci gaba da biyawa yara dalibai kudin makaranta, kudin jarabawar kammala sakandare da kuma daukar nauyin dalibai nauyin karatunsu a kasashen waje ba tare da la’akari da dan wane ko sai wane ko wace ba,to mutane su shirya tsaf domin zaben PDP a kowane irin mataki idan lokacin zabe yazo.
Shugaban na PDP ya kuma kara fadakar da jama’a da suka isa kada kuri’a da su shirya domin zaben shugabannin kananan hukumomi a lokacin da aka shirya gudanar da zaben domin Gwaji kafin zaben Gwamnoni da na shugaban kasa da yan majalisun tarayya da na Jiha, wanda a cewarsa hakika zai ba PDP kwarin ci gaba da ayyuka a kowane fannin inganta rayuwar bil’adama.
Honarabul Abubakar Tsoho ya kuma bayyana gamsuwa da irin sakon jagorancin shugabannin PDP na Jihar Katsina tun daga kan shugaban PDP na Jiha Alhaji Salisu Yusuf Majigiri, Alhaji Yakubu Lado da kuma tsohon Gwamnan Jihar Katsina Barista Ibrahim Shehu Shema bisa jagoranci nagari da suke yi wa jam’iyyar.
Ya kuma mika godiyarsa da yayan Jam’iyyar PDP bisa jajircewar da suka yi wajen zabensa a matsayin shugaban PDP na karamar hukumar Bakori.
Sai ya yi kira ga masu zabe wato deligat da a ranar Talata su tabbatar sun zabi Alhaji Salisu Yusuf Majigiri saboda nagartarsa da kuma cancanta domin shi ne wanda ya fi kowa cancanta a ci gaba da zama shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Katsina saboda kwazonsa da gogewa tare da aiki tukuru