Home / Ilimi / Makarantar Yan Mata Ta Jeka Dawo Ta Shinkafi Ta Lashe Gasar Suleiman Shu’aibu

Makarantar Yan Mata Ta Jeka Dawo Ta Shinkafi Ta Lashe Gasar Suleiman Shu’aibu

Imrana Abdullahi Daga Shinkafi
A kokarin ganin an samu manyan Gobe masu ilimi da sanin yakamata a cikin al’umma yasa Sarkin Shanun Shinkafi na farko Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, ya shirya gasar mahawara tsakanin makarantun Yan mata na Jeka ka Dawo da ke karamar hukumar Shinkafi
A jawabinsa da ya gabatar jim kadan bayan kammala gasar Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, ya bayyana dalilin shirya wannan gasar da cewa an yi ne domin kara wa dalibai matasa manyan gobe himmar yin karatu da nufin su bayar da gudunmawarsu wajen ciyar da al’umma gaba.
 “Hakika Dokta Bello Muhammad Matawalle Gwamnan Jihar Zamfara na matukar farin ciki da irin wannan gasar da ake yi a tsakanin daliban makarantun Sakandare”.
Malam Nasiru Garba, ya bayyana makarantar Yan mata ta Jeka ka dawo da ke garin Shinkafi a matsayin wadanda suka yi na daya da maki 822 wadanda suka goyi bayan cewa ya dace Gwamna Muhammadu Bello Matawalle a sake zabensa karo na biyu, da aka ba su kyautar Keken Dinki sabo fil.
Sai kuma Karamar makarantar Sakandare ta Yan mata ta Jeka ka Dawo da ta zo ta biyu da maki 752 da suka tattauna a game da batun sake zaben Gwamna Muhammadu Bello Matawalle, an ba su kyautar kudi naira dubu Talatin
Sai kuma Makarantar Sakandare ta al’umma da ke garin Shinkafi da suka zo na uku da maki 698 da aka ba su kyautar naira dubu Ashirin.
A lokacin gudanar da gasar an samu Alkalai biyu da mai kula da lokaci sai mai aikin sa ido guda daya a game da gasar.
Taron gasar dai ya kayatar kwarai da gaske domin jama’a da dama sun bayyana farin cikinsu a wajen gudanar da gasar.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.