Home / Labarai / A Ci Gaba Da Rungumar APC Domin Kawo Gyara – Durunguwa

A Ci Gaba Da Rungumar APC Domin Kawo Gyara – Durunguwa

Daga Imrana Abdullahi
An yi kira ga daukacin al’umma Maza da Mata da suka Isa Jefa kuri’a da su ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga jam’iyya APC domin kawo gyara a kasa baki daya.
Tsohon dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna karkashin tutar jam’iyyar Dokta Abdulmalik Durunguwa ne ya yi wannan kiran a wani taron da aka kira na daukacin magoya bayansa na hakika tun lokacin da ya yi takarar neman jam’iyyar ta tsayar da shi takarar Gwamna karkashin APC.
“Muna yin amfani da wannan damar da kuka taru wakilan al’umma daga kowace karamar hukuma mutane biyar biyar domin yin wakilci ga sauran mutanen da suka yi tafiyar mu a lokacin zaben neman kujerar Gwamnan Jihar Kaduna, muna cewa ayi hakuri domin yadda abubuwan suka kasance ba haka aka so ba”.
Durunguwa ya ci gaba da cewa ina yin kira ga jama’a da su rungumi tafiyar mai neman Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC Bola Ahmad Tunubu domin a cimma nasarar da kowa ke bukatar samu.
“Hakika idan aka kafa Gwamnatin APC a Jihar Kaduna lamarin ba zai kasance kamar yadda ake yi a halin yanzu ba duk wanda ya bayar da gudunmawa tun daga matakin akwati za a saka masa, kuma an Sanya kofin gasa tun yanzu ga duk akwatin zaben da aka samu kuri’ar APC kashi Kasa’in akwai gagarumar kyautar da za a yi wa wannan akwatin zabe, ni da kaina zan shige gaba sai an yi ruwan abubuwan arziki kowa ya samu”, inji Durunguwa.
Magoya bayan a jawaban da suka yi daban daban sun bayyana Abdulmalik Durunguwa a matsayin mutumin jama’a mai nuna kauna da kishin jama’a a koda yaushe.
Magoya bayan suka ce su ne da kansu suka shirya wannan taron na jama’a kalilan da a nan gaba za a gudanar da babban taron dimbin jama’a magoya baya.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.