Home / Labarai / A Daina Fadin Abin Da Ba Shi Ake Aikatawa Ba – Makarfi

A Daina Fadin Abin Da Ba Shi Ake Aikatawa Ba – Makarfi

Mustapha Imrana Abdullahi

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Ahmad Muhammad Makarfi, ya yi kira ga daukacin al’umma baki daya da su daina fadin abin da ba shi suke aikatawa ba.

Sanata Ahmad Muhammad Makarfi ya bayyana hakan ne  lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna jim kadan bayan kammala Sallar Idin layya ta ba na da aka yi a filin Idin makarantar Kpital da ke cikin garin Kaduna.

Sanata Makarfi ya ci gaba da cewa duk da irin halin da ake cikin na wahalhalun rayuwa da kuma halin rashin tsaro a kasa da talauci da Yunwa amma jama’a sun jajirce wajen yin addu’o’I domin kasa ta ci gaba.

“Don haka muke jajircewa da a ci gaba da aiwatar da aikin ciyar da kasa gaba duk da kasancewar hali ne mai wahala ga kuma lokacin Sallah da ya zo”.

Tun da farko Limamin da ya jagoranci Sallar Idin Imam Mohammad Khalil kira ya yi ga daukacin al’ummar musulmi da su ci gaba da bin karantarwar addinin Islama sau da kafa tare da cika dukkan sharuddan da musulunci ya tanada game da idin babbar Sallah.

Limamin ya yi bayani mai tsawon gaske game da irin karantarwar addinin Islama kan taimakawa da abin layya r da mutum ya samu ikon yi.

Da ya bayar da misalin cewa wanda ya yi layya zai raba kashi uku ya yi kyauta da wanda ya fi kyau daga ciki sai ya yi sadaka da wani kaso dayan kuma ya ci da iyalinsa, ya kuma fadakar game da Sada zumunci da ya bayyana shi a matsayin al’amari mai dimbin falala.

About andiya

Check Also

Senator Yar’adua Donates Books To Schools In 11 LGAs

By Lawal Gwanda Senator Abdul’aziz Musa Yar’adua of Katsina Central Senatorial District has donated assorted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.