Home / Labarai / A Gaggauta Binciko Wadanda Suka Kashe Malami A Jihar Zamfara – Yan kungiyoyi

A Gaggauta Binciko Wadanda Suka Kashe Malami A Jihar Zamfara – Yan kungiyoyi

Gwamnatin tarayya ta kashe batun yan sandan Jihohi 

An Yi kira ga Gwamnatin Jihar Zamfara karkashin Dauda Lawal da ta hanzarta gudanar da bincike a game da kisan da aka yi wa Malamin addini da aka yi wa yankan rago.

Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi memba a kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty kuma babban Darakta na kasa a kungiyar warware matsalolin rikice rikice ya yi wannan kiran.

Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya ci gaba da bayanin cewa lallai ya zama wajibi ga Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Dauda Lawal ta gudanar da ingantaccen kyakkyawan bincike na gaskiya game yadda aka kashe wannan Malami mai daraja da dimbin magoya baya, amma aka yi masa yakan Rago haka kawai.

“Mun Sanya wata tawagar manema labarai da suka kware a fannin bincike da suje su kuma gudanar da bincike a kan yadda lamarin yake a binciko gaskiya, duk abin da binciken ya nuna za mu ga ko ya yi dai- dai da na Gwamnati idan kuma na mu ya yi sabani hakika za mu ta fi kotu domin a samu hukuncin da ya dace”.

Shinkafi, ya kara da cewa idan sun je kotun za a nemi a biya diyyar ran bawan Allah da aka kashe. Da wanda aka kashe a garin kauyen Yan doto a karamar hukumar Tsafe, domin bayanan yan uwan sa da yayansa duk bayan an kama su an tursasa su cewa su fadi cewa wai ya na tare da yan Ta’adda wato yan bindiga.

Da wannan ne muke yin kira ga Gwamnatin tarayya da ta kashe batun yan Sandan Jihohi domin “ana iya yin amfani da Yan Sandan Jihohi a rika kashe mutane, indai har hakan ta tabbata wadanda ba yan Sanda ba suka yi wannan to, komai zai iya faruwa kenan. Domin wadanda suka aikata wannan har gida suka je suka yi masa yaudar cewa an san shi mai son zaman lafiya ne ya je ya sasanta wani abu ya hanyar yin fatawa a kan wani abu amma suka dauke shi suka ta fi da shi daji suka yanke yankan Rago, hakika wannan ba shi da kyau domin tashin hankali ne kwarai matuka da bai dace ba ko kadan, saboda haka ne muke cewa lallai aika aika irin wannan duniya ba za ta bar wannan ba sam ko kadan”.

“Don haka ne muke yin kira ga daukacin al’ummar duniya  da su shigo cikin wannan lamarin da niyyar taimakawa mutanen Jihar Zamfara bisa halin da suka tsinci kansu a ciki. Kuma muna yin kira ga Gwmatin tarayya da ta shigo cikin wannan kwamitin na bincike domin a gani musababbin wannan lamarin na aika aikar.Domin idan mutane na daukar doka a hannunsu lallai zama ba zai yi kyau ba za a koma zaman jahiliyya ba doka da oda”.

Gwamnatin Jihar Zamfara fa ta kafa rundunar Askarawa ne domin kare mutane daga ayyukan yan Ta’adda masu satar mutane da Dabbobi suna karbar kudin fansa.

“Mun fitar da sanarwar bayan taron da muka yi ne a Abuja da muka ba Gwamnatin jihar Zamfara damar nan da sati daya da a gaggauta yin bincike a gano musabbabin wannan matsalar da ke neman ta cinye kasa domin jinin wannan mutum ba zai ta fi haka nan ba don in ma Gwamnatin jihar Zamfara ba ta yi komai ba to, Allah zai yi wani abu. Da haka ne nake yabawa kungiyar Izala ta Jihar Zamfara a bisa matakin da aka dauka kada ayi tashin hankali kada kowa ya zagi wani kuma kada ayi Zanga Zanga su bari kungiyoyin kare hakkin bil’adama za su dauki matakai kuma mu muna nan muna daukar matakai kuma na Sani ita kanta Gwamnatin jihar Zamfara za ta dauki mataki domin har ta fara dauka ma sai dai idan mun ga matakan ba su yi mana ba za mu ta fi kotun ECOWAS mu nemi kadin wannan kuma mu garzaya kotun duniya ta ICC mu tabbatar kashe wannan mutum ya zama izina ga dukkan wanda yake da matsayi a Najeriya”, inji suleiman S Shinkafi.

“Domin dauki dai dai da kisan jama’a ba kan kado idan Gwamnati ba ta dauki mataki ba hakika za mu dauki laifin mu Dorawa Gwamnati mu ce ita ke Sanya su, amma a halin yanzu duk muna jira ne har sai kwamitin binciken da Gwamnati ta sanya ya fitar da rahotonsa, kuma mu na mu kwamitin binciken suna nan suna yin binciken tun shekarar jiya”.

Bayan haka muna kira ga Gwamnan Jihar Zamfara Dauda lawal da ya yi gaggawar sauke Konal Yandoto daga mukaminsa na Kwamandan wannan sannan ya rushe wadannan yaran da ya dauka da za su tsare lafiyar jama’a da dukiyarsu tare da rayuwarsu. Hakika rushe su da sauke wannan zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali na cewa Gwamnatin jihar Zamfara ta dauki mataki kuma ba tare da ita aka yi wannan abu ba.

Kuma muna yin kira ga Gwamnan zamfara da ya yi gaggawar sauke kwamishinan tsaro ko S A na harkar tsaro idan har ya na da shi

Domin faruwar wadannan abubuwa na kashe rai idan a kasashen waje aka yi shi inda ake kare hakkin bil’adama, wallahi wadannan mutanen da na lissafa ba sai an ce masu su sauka ba, su da kashin kansu za su sauka a yi bincike kamar yadda ya dace don haka Kanar Yadoton nan ya dace ya sauka ayi bincike a tabbatar an zakulo wadanda suka aikata wannan ko su yan bangan ne ko Askarawa ne da Gwamna ya kafa. Kuma ta yaya za a ce wai yan banga ne? hakan ma bai taso na ko kadan don haka kawai a kamo wadanda suka aikata aika aikar nan a hukunta su kawai.

Ina magana da yawun dukkan yan kare hakkin bil’adama da kungiyoyi da muka yi taro saboda haka ba za mu lamunci wannan ba  , mun cimma matsayar cewa jinin mutumin nan ba zai ta fi a banza ba don haka muke ba Gwamna shawara a matsayinsa na shugaba ya dauki kwakkwaran mataki kada ya bari wadansu masu son zuciya su lalata mashi Gwamnatinsa. Ko a zamanin da can ba a rika yin yankan rago ba balantana a wannan lokacin da Dimokuradiyya ta ci ga ba sai a rika samun irin wannan da aka yi Gwagwarmaya aka zabe ku ba Dare ba rana sannan a wannan yanayi ne za a dauki malamai a rika kashe wa haka kawai duk da sune ke zuwa suna yin wa’azin Mako Mako a yanka shi, to ina ga sauran malamai

Kuma kira na karshe shi ne ayi gaggawar biyan diyya na mutumin nan da aka kashe kuma a hanzarta Dakatar da Yandoto a kuma Dakatar da wannan hukuma domin hakan zai kwantar wa da jama’a hankali.
Muna kuma son mutanen kasashen waje da muka rubutawa takardun neman kare hakkin bil’adama da su yi gaggawar daukar mataki idan sun ga takardun mu

Da fatan Allah ya jikan wanda ya rasa ransa da duk wadanda aka kashe kuma Allah ya ba kungiyar Izala reshen Jihar Zamfara da kasa baki daya  hakurin wannan babban rashin

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.