Home / Labarai / A Kalla Mutane 78 Sun Mutu A Harin Bam 

A Kalla Mutane 78 Sun Mutu A Harin Bam 

 Imrana Abdullahi
Rahotannin da kw  fitowa daga kasar Lebanon na cewa a kalla mutane 78 sun rasa ransu a wani harin Bam da aka kai a kasar.
Rahotannin suna cewa a halin da ake ciki mutane na ta neman yan Uwansu sakamakon tashin Bam din da aka samu.
Firayim ministan Lebanon Hassan Diab ya shaidawa manema labarai cewa wadanda suka aikata wannan aikin za su yabawa Aya zakinta domin sa a yi masu hukunci dai dai da abin da suka aikata.
Shugaban Kasar Amurka Donald Trump a wani jawabin da ya yi wa duniya ya jajantawa daukacin mutanen kasar, tare da yin alkawarin taimakawa sakamakon Bam din da ya tashi da a cewarsa ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da raunata wadansu mutane masu yawa.
Daga cikin wadanda suka rasa rayukan nasu kamar yadda rahotanni ke cewa akwai wadansu manyan mutane, inda bam din ya tashi a cikin wata mota.
Wadansu kafafen yada labarai na yanar Gizo na cewa ana ganin harin bam din kamar wani al’amari ne na yakin da ke faruwa a kasar Syria.
Kara da kuma tsananin karfin fashewar ta girgiza kass da kuma rusa wadansu wunduna da kafofi a babban birnin kasar beirut da ke kasar Lebanon.

About andiya

Check Also

Tinubu Appoints Silas Ali Agara DG NDE

By Ibraheem Hamza Muhammad President Bola Ahmed Tinubu has approved the appointment of Honourable Silas …

Leave a Reply

Your email address will not be published.