Home / News / A Zabi Asiwaju Bola Ahmad Tinubu – Injiniya Kailani Muhammad

A Zabi Asiwaju Bola Ahmad Tinubu – Injiniya Kailani Muhammad

Daga Imrana Abdullahi Daga Abuja
Wani jigo a jam’iyyar APC Injiniya Dokta Kailani Muhammad ya yi Kira ga daukacin yan Najeriya da su himmatu domin zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmad Tinubu domin kasa ta inganta.
“Saboda irin wannan dalilin ne na ci gaban kasa ya sa muke fadakar da dimbin jama’a abin da ya dace da nufin kasa tare da al’ummarta su samu nasarar da kowa ke bukata”, inji Kailani.
Injiniya Kailani Muhammad ya yi wannan kiran ne na jama’a su zabi Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2023 mai zuwa ne a garin Abuja lokacin da yake ganawa da manema labarai.
“Idan jama’a za su iya tunawa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya taka rawar gani sosai a lokacin da zama Gwamnan Jihar Legas kuma kamar yadda kowa ya Sani an ga dimbin ci gaba mai ma’ana da a yanzu kusan kowa ke yin misali da shi.
“Hakika muna yin mamaki kwarai irin yadda wadansu yayan jam’iyyar APC masu rike da mukamai a matakin Gwamnatin Jiha suke yin wadansu kalamai da za a rika ganin laifi ki gazawar Gwannatin da suke ciki, don haka muke fadakar da jama’a su kara hanzartawa wajen zura idanu da kuma lalubo masu wannan akida da ke kama da koma baya”.
Injiniya Kailani Muhammad ya kara da cewa bari in fito maku fili, ” kalaman da Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i ke yi game da batun man fetur ba mu ga ne nufinsa ba domin wanda ke cikin Gwamnati kuma ya na wadancan kalamai irin na sa”, inji Kailani Muhammad.
Za mu kawo maku cikakkun bayanan da aka yi a lokacin taron manema labaran da Injiniya Kailani tare da jama’arsa suka kira a garin Abuja.

About andiya

Check Also

Aliyu Sokoto tasks cabinet on transformation drive, ‘ be committed and sincere 

  By Suleiman Adamu, Sokoto SOKOTO state Governor Dr Ahmed Aliyu Sokoto has tasked members …

Leave a Reply

Your email address will not be published.